Header Ads

An Sako Fasinjoji Uku Na Jirgin Kasan Abuja-Kaduna

 


Rahotanni daga jihar Kaduna a arewacin Najeriya sun ce ƴan bindiga sun sake sako mutum uku daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin mutanen uku ya tabbatar wa da BBC labarin, inda ya ce an sako su ne a ranar Litinin da rana.

Fasinjojin da aka saka ɗin sun haɗa da maza biyu da mace ɗaya.

A lokacin da yake tabbatar wa BBC labarin, ɗan uwan ɗaya daga cikinsu ya ce suna kan hanyar zuwa asibiti don duba lafiyar ɗan uwan nasu.

Sakin nasu na zuwa ne kwana ɗaya bayan da ƴan bindigar suka saki wani bidiyo da ke nuna yadda suke zane maza daga cikin fasinjojin.

Sai dai babu wani cikakken bayani zuwa yanzu kan sharuɗɗan da aka cika kafin sakin nasu.

A ranar 28 ga watan Maris ɗin 2022 ne masu tayar da ƙayar baya suka kai wa jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna hari da daddare.

Kuma tun wannan lokacin, wannan ne karo na biyar da suke sakin fasinjojin da kaɗa-kaɗan.

A yanzu saura da aka sako fasinjoji uku, lissafi ya nuna saura mutum 40 suka rage a hannun ƴan bindigar.

Su waye aka sako?

Wadanda aka sako din sun hada da maza biyu da mace daya.

A lokacin da abokinmu Yusuf Tijjani ya kai ziyara da gidan ɗaya daga cikin waɗanda aka sako ɗin, ya ce tuni wajen ya cika da ƴan uwa da abokan arziki masu taya murna.

A bidiyon da masu tayar da ƙayar bayan suka saka ranar Asabar da ke nuna yadda ake dukan fasinjojin, ɗaya daga cikin waɗanda aka sako ɗin shi ne Barista Hassan Usman, wanda suka bai wa dama ya fara magana sanye da shuɗiyar riga a jikinsa.

Ya yi bayanin ne kan yadda aka sace su da kuma bayyana cewa gwamnati ta gaza kubutar da su.

A bidiyon, ya yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya irin su Amurka da Ingila da Faransa su taimaka su ceto su, yana mai cewa “gwamnatin da ke da hakki ta karbo mu ta gaza”.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar da suka sace su ba su yi niyyar tsare su a hannunsu na lokaci mai tsawo ba.


No comments

Powered by Blogger.