Header Ads

Gwamnati ta fara binciken Ministar Agaji kan umarnin zuba naira miliyan 585 a asusun wata ma'aikaciya - Idris

Ministan Yaɗa Labarai da wayar da kan jama'a 

Sakamakon ƙorafe-ƙorafe da rahotannin zargin da ake yi wa Ministar Harkokin Agaji da Jinƙai, Dakta Betta Edu, Gwamnatin Tarayya ta fara binciken yadda aka zuba naira miliyan 585.2 a asusun ajiyar wata ma'aikaciyar gwamnati, bisa umarnin ita ministar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a ranar Lahadi cikin wata sanarwa ga manema labarai.

Ita dai Minista Betta Edu, ta na ci gaba da shan ragargaza daga ko'ina a faɗin ƙasar nan bayan an fallasa yadda ta bada umarnin a zuba zunzurutun kuɗi har naira miliyan 585.2 a cikin asusun banki na wata ma'aikaciyar gwamnati, wadda ita ce akawu mai kula da Kuɗaɗen Tallafin Marasa Galihu a ma'aikatar.

Dakta Edu ta fitar da wasiƙar bada umarnin zuba wa ma'aikaciyar kuɗin ne ga Akanta Janar na Tarayya a cikin Disamba, 2023, inda ta rubuta cewa a zuba kuɗin cikin asusun, duk kuwa da cewa yin hakan ya karya doka.

Duk da cewa Akanta Janar ya ce mata yin hakan karya doka ne, amma ya amince an biya kuɗin cikin aljihun asusun ma'aikaciyar, wanda ministar ta ce a zuba mata kuɗin.

Wannan ne ya jawo ce-ce-ku-ce da nuna damuwar da har Gwamnatin Tarayya ta gaggauta fara bincike. 

Sai dai ita kuma Edu ta ce ba ta aikata wani laifi da ya saɓa wa doka ba, duk kuwa da cewa akwai tambayoyin da ma'aikatar ta ya kamata ta amsa, haka shi ma ofishin Akanta Janar ɗin akwai tambayoyin da ya kamata ya amsa domin warware zare da abawa.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Idris ya ce yanzu haka gwamnati ta fara bincike, sannan kuma ta gamsu da yadda 'yan Nijeriya su ka nuna damuwar su dangane da wannan zargi da ake yi wa ita ministar.

Ya ce: "Mu na sane da dukkan ce-ce-ku-cen da ake ta yi kuma mu na tabbatar wa da 'yan Nijeriya cewa gwamnati ta ɗauki wannan batu da muhimmancin gaske."

Ya ci gaba da cewa Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu, ba ta gudanar da ayyukan ta cikin ƙumbiya-ƙumbiya.

Ya ce gwamnatin za ta tura kuɗaɗe a inda ya dace kai-tsaye, domin ayyukan biyan buƙatun 'yan Nijeriya.

Haka nan kuma Idris ya yi kira tare da bada shawara ga jama'a da cewa a maida hankali wajen samun sahihan bayanai daga Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da ya ke jagoranta.

Hakan a cewar sanarwar sa, ya na da nasaba da ganin yadda ake ta yaɗa labarai da bayanai marasa tushe balle makama da su ka shafi Gwamnatin Tarayya.

No comments

Powered by Blogger.