Header Ads

TA YA YA ZAN GANE MACE TA GARI?



Daga Fatima Adamu Tinja Fika, Yobe


Yana da kyau ka zama mai tarbiyya da tsari a rayuwarka don yi wa ‘Ya’yanka tsani na samar da al'umma mai nagarta. Ta hanyar samar musu da uwa ta gari, domin Mace Ingantacciya ita ce Matar da kowane Namiji zai so ya sami zuriya da ita, Ma'ana ya aure ta.

Yadda za ka gane Mace ta gari.

1.   ZAKA GANTA KAMILA.

Mace kamilalliya ita ce wadda take me kamun kai, ba ta shiga hayaniya, za ka same ta ko da cikin ‘Yan’uwanta Mata ba ta da rawar kai bare a gun Maza.

KAMILALLIYAR MACE;  Za ka gan ta ba ta da shige wa maza ko da Muharramanta ne, akullum in ka ganta da Namiji da ya zama dole sai an gansu saboda alakar karatu ko aiki ko wata hujja ta daban, dik da ya zama dole to za ka ganta a tsorace,tana kaffa-kaffa dasu.

Matakin farko da Namiji ya kamata ya fara dubawa yayin Zabar Macen da zai aura shi ne;  Ya fara duba ya Macen take, shin tana da kamun kaine ko bata dashi, Wannan hanyar shi  ya kamata namiji ya bi don tabbatar da cewa ita Mai kamun kai ce,domin tabbas Matar aure mai kamun kai ake nema. 

2.    BA TA YAWAN SURUTU.

Mace Mai kamewa da karancin magana tana da tasiri kwarai a lokacin da ake batun aure dama bayan auren.

Sau tari matsalar da ake samu na shiga aikin assha tsakanin abokin miji ko kuma wani danuwan Mijin, tana fara kulluwa ne ta yadda Mace take sakin jiki ta yi ta surutai marar fasali, To daga nan sai a gane ba ta da tsada,da an yi mata karamar magana za ta fada.

Tana tutananin in ta shiga dandazon maza ta daga muryarta da zakewa shi ne zai janyo hankalin Namiji kan ta,wanda sam ba haka bane.

Surutu barkatai alamu ne na rashin kamun kai, Macen kwarai ba a santa da daga harshe ba, ko da a cikin‘Yan’uwanta mata ne bare kuma maza. 

3.  ZAKA GANTA ME KUNYA. 

A kwai alamomi da suke nuna lallai wannan bata da kunya ciki akwai;  ciye-ciye a kan hanya ko gaban samari.

Mace Mai ciye-ciye da rashin kimtsi,ko ga sa’anninta mata ba ta farin jini bare maza, zaka ga tana taunar cingam agaban mutanen da bai dace ba, duk wannan alamun rashin kunyane ga mace, ko ta furtama banzan magana, sannan idan tazo gaban Maza zaka ga tana wani karairaya da rankwasa,da kuma kashe murya, ko ta dinga tigar rawa  agun biki, Hatta acikin Maza bata kunyar yin rawa. To wannan dik yana cikin alamomin da zaka gane mace bata da kunya.

Kunya na da matukar tasiri a rayuwar 'Ya Mace, Domin Mace da kunya da kara da kawaici aka santa ba da rashin kunyaba, Shi yasa Maza masu wayo basa taba auren Mace marar kunya ko dan tarbiyyar 'Ya'yansu.

 Sannan Mace marar kunya ba ta farin jini wajen Al'ummar da suke da mutunci, Hatta a gidan aure in har yarinya ta zama marar kunya ba a taba samun jituwa da iyayen miji ko danginsa. 

4.   BATA DA YAWAN KALLO.

A kallo kadai a na iya gane Mace mai kunya da rashinta. Yadda mace za ta kafe Namiji da ido yana nuna kunyarta da rashinta musamman idan yana wata Magana. Mace an fi sanin ta da risnawa. 

5.   TANA DA AJI.

Zaka ganta bata da girman kai Amma tasan darajar kanta, Ina nufin tana da jan'aji,Domin dik Mace ta kirki tana da jan'aji da kamewa,bata zamar da kanta arha ta yadda kowanne Namiji ya kira ta batare da tantancewa ba taje, Ma'ana kowa yake bukatar jin hira da ita taje,ko wannan yaqirata ta daga,wancan ya tsayarda ita ta tsaya da sauransu, Ita kowane Shararma kulawa take,da wanda ya dace da wanda bai daceba. 

To ita Mace ta gari tana da jan'aji da kamewa ta wannan bangaren,baza kuma aqira hakan da girman kaiba.

6.  BATA SA KAYAN DA ZAI BAYYANA SURARTA TA FITA.

A koda yaushe zaka ganta cikin shiga ta kamala ta'addinin musulunci,Domin Mace ta gari bata taba yadda wanda ba Muharramanta suga koda wani Sashi/bangare na jikinta.

Amma Mata a yau suna tunanin bayyana tsiraicinsu shi ne hanyar da za su iya janyo hankalin Namiji garesu, Har ya gane kyan wani bangare na jikinsu da zai kai su ga aure.Ko kuma wata wayewa ce dacigaba saka matsattun kaya.

Bayan kuma Manzon Allah(S) Ya tsinewa mata masu irin shiga Mai nuna tsiraicinsu,kuma Yace; "Baza suji koda qamshin Aljanna ba".  Ha'ilau "Manzon Allah(S) Yace; Idan kukaga khasiyatun Ariyatt, Ku tsine musu,domin awurin Allah sudin tsinanannu ne". Shin me zakayi da Macen da Allah da Manzon sa suka tsine musu, kaga ka dauko larura gidan ka kenan, Sannan ina makomar tarbiyyar 'Ya 'yanka suke ?!.

To wannan babban kuskure ne ga Namjin da zai dauki wannan Amatsayin Matar da zai aura. 

Ya kai dan'uwa mai daraja, kasani cewa; Macen da ke sanye da Suturar mutunci ake nema a Aura ba ballagaza da ta gama nuna kanta a titi ba.

No comments

Powered by Blogger.