Header Ads

Rukunin karshe na sojojin Faransa sun bar jamhuriyar Nijer tare da kwashe kayansu

Rukunin sojojin Faransa na karshe a ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2023 na shiga cikin wani jirgin soja na Faransa domin barin Nijer a wani sansanin sojojin Faransa da aka mika a hannun sojojin kasa na Nijeriya.

Rukunin karshe na sojojin kasar Faransa sun bar jamhuriyar Nijer a ranar Juma'a, wanda hakan ya kawo karshen yakin da suke yi da masu ikirarin jihadi a cikin shekaru sama da goma a yankin Sahel da ke yammacin Afirka.

Kamar yadda wani rahoto na kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ya nuna, sojojin sun tafi tare da barin daruruwan sojojin Amurka da wasu na kasar Italiya da Jamus, kamar yadda AFP ta ruwaito.

Faransa ta bayyana cewa za ta kwashe duka sojojin ta da ba su gaza 1,500 ba da matuka jiragen ta daga Nijer bayan da sabbin janarorin Faransar, wadda ita ce ta yi mulkin mallaka ga Nijer, suka nemi ficewar bayan gudanar da juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli a Nijer.

Wannan shi ne karo na uku a cikin kasa da watanni 18 da sojojin Faransa ke kwashe kayansu tare da barin kasar da ke yankin Sahel bayan gudanar da juyin mulki a sauran kasashen da Faransar ta yiwa mulkin mallaka na Mali da Burkina Faso.

Duka kasashen uku na yaki da masu ikirarin jihadi a arewacin Mali inda fada ya barke a shekarar 2012 tare da yaduwa, sai dai dangantaka tsakaninsu da Faransa ta yi tsami bayan da aka gudanar da juyin mulki a jere a yankin.

Sojojin na Faransa na karshe sun tashi daga babban birnin kasar Niamey a cikin jiragen sama biyu, kamar yadda wani dan jaridar AFP ya shaida. 

"A ranar yau ake kawo karshen ayyukan sojojin Faransa a yankin Sahel." Kamar yadda wani sojan Nijer, Laftanar Salim Ibrahim ya bayyana.

Wasu sojojin Faransa 1,000 sun tsaya a makwafciya Chadi, inda Faransa ke da sansaninta na yaki da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel, amma yanzu ba ta a cikin manyan kasashe uku da ke yaki da masu tsatstsauran ra'ayin.

Ibrahim ya bayyana cewa ficewa daga Nijer din, wanda aka fara a watan Oktoba, ya hada da kwashewa a jiragen sama har sau 145 da kuma ta kasa har sau 15.

Sojojin na Faransa sun shaidawa AFP cewa ba su bar kayayyakin su ba amma an bar gine-gine.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, a watan Satumba ya bayyana cewa zai kwashe duka sojojin Faransa daga Nijer zuwa karshen shekara.

A Nijer, mafiyawancin sojojin Faransa an ajiye su ne a wani sansanin sojin sama da ke Niamey, yayin da kadan kuma suke tare da sojojin Nijeriya a kan iyakar Mali da Burkina Faso, inda aka yi imanin cewa masu ikirarin jihadi wadanda ke da alaka da Al-Ka'ida da kuma Islamic Jihad ke gudanar da ayyukansu.

Mahukunta a Nijer dai suna bukatar shekaru har zuwa uku ne domin su mika mulki zuwa fararen hula.

Shugabannin soja na Nijer a farkon wannan watan sun bayyana cewa za su kawo karshen ayyukan tsaro na Tarayyar Turai guda biyu a kasar.

No comments

Powered by Blogger.