Header Ads

Badakalar sauya fasalin naira: HURIWA ta bukaci a kamo tare da hukunta dan'uwan Buhari

Takardun Naira da aka sauya wa fasali bara

Kungiyar marubuta masu fafutikar kare hakkin dan Adam ta Nijeriya (HURIWA) ta yi kira da ba da bata lokaci ba a kamo tare da hukunta Tunde Sabiu, wanda ya ke dan uwa ne ga tsohon shugaban kasa Buhari, sakamakon rawar da ya taka wajen sauya fasalin naira ba da dadewa ba ba tare da cikakken izini ba.

Kungiyar ta yi Allah wadai da da amincewar sauya fasalin nairar, inda ta bayyana cewa amincewar ta zo ne daga Tunde Sabiu 'Yusuf' maimakon daga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mai bincike na musamman na babban bankin Nijeriya (CBN) da sauran makamantansa, Jim Obazee, ya bayyana a cikin rahoton karshe da ya mika ga shugaban kasa cewa amincewa a sauya fasalin nairar ba daga tsohon shugaban kasa ya zo ba sai dai daga mai taimakawa shugaban kasa ne, Sabiu Tunde 'Yusuf.

Kamar yadda ya ke a cikin wani rahoton The Guardian, HURIWA a cikin wani jawabi wanda mai mai kula da al'amurranta na kasa, Kwamared Emmanuel Onwubiko, ya sawa hannu, ta bayyana damuwa a kan abinda suka kira karya ka'ida inda suka dage cewa sai an yi gamsasshen bayani kan rawar da Sabiu ya taka wajen sauya fasalin kudin.

HURIWA ta bukaci ba da bata lokaci ba a kamo tare da hukunta Tunde Sabiu domin rawar da ya taka a cikin badakalar.

"In har za a iya tunawa a cikin wata wasika mai kwanan wata 28 ga watan Yuli na shekarar 2023, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Obazee, wanda ya ke tsohon babban sakataren kwamitin rahoto kan kudi na Nijeriya ne, a matsayin mai bincike na musamman na babban bankin Nijeriya (CBN). Kamar yadda rahoton ya nuna, Sabiu da Godwin Emefiele, tsohon shugaban babban bankin Nijeriya (CBN) wanda ke da matsaloli, sun yi aiki tare domin su tabbatar da sauya fasalin naira. Dan uwan tsohon shugaban kasar shine Sabiu." Kamar yadda HURIWA.

Har wa yau, kungiyar ta nuna damuwa dangane da ayyukan tsohon ministan jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, dangane da aikin da ya shafi jiragen saman Nijeriya.

HURIWA ta yi ikirarin cewa Sirika ya yi cuwa-cuwa ta hanyar nuna jirgin da aka yi wa fenti a matsayin jirgin saman kasa, domin ya yi cuwa-cuwa ga 'yan kasa.

HURIWA ta tabo kashe kudaden da ba kan ka'ida suke ba wandanda suka shafi Sirika wanda ya hada da kashe dalar Amurka 600,000 domin zana alama da sayen motocin kashe gobara wanda ke tattare da ayar tambaya.

Bayan haka HURIWA ta bukaci gamsasshen bayani daga Sadiya Umar Farouq, tsohuwar ministar ayyukan jin kai, cigaban al'umma da kula ko kare da annoba, dangane da kudaden da aka ware domin ayyukan cigaba, musamman shirin ciyarwa a makarantu. Kungiyar ta lissafo zarge-zarge da suka hada da rashawa, cin amanar ofishi da kuma rashin kula da kudade a lokacin ta, inda suka yi kira da ba da bata lokaci ba a kama ta kuma hukumar tsaron farin kaya (DSS) da hukumar yaki da rashawa da zagon kasa ga tattalin arzukin kasa (EFCC) su bincike ta.

No comments

Powered by Blogger.