Header Ads

Kiristocin Siriya sun soke bukukuwan kirsimeti domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa

Wasu 'yan kasar Siriya na rera wakokin kirsimeti a coci

Ba zagaye a kan tituna saboda kirsimeti a biranen Siriya, inda manyan cocina suka takaita bukukuwa domin gudanar da addu'o'i saboda nuna goyon baya ga Falaadinawa da ke fuskantar wahalhalu a Gaza.

"A Falasdinu, inda aka haifi Yesu kiristi, mutane suna cikin wahala." Kamar yadda Syriac Catholic Archbishop na Aleppo, Mor Dionysius Antoine Shahda, ya shaidawa AFP.

Birnin da ke gabashi na Azizia waje ne da mafiyawanci ya ke da kasuwa da ke cika domin bukukuwa da kuma katuwar bishiyar kirsimeti, yayin da ake yiwa titunansa kwalliya da haske da sauran kwalliya.

Amma a wannan shekarar babban filinsa ba kowa yayin da kuma babu kwalliyar kirsimeti.

"A Siriya mun soke dukkan bukukuwanmu da tarukan cin abincinmu a Maja'mi'unmu domin nuna goyon baya ga wadanda hare-haren bom ya shafa a Gaza" sanadiyyar sojojin Isra'ila, kamar yadda Shahda ya bayyana.

Maja'mi'ar Siriya ta Katolika ba ita kadai ba ce, har da shugabannin manyan majami'o'in Siriya - the Greek Orthodox, Syriac Orthodox da kuma Melkite Greek Catholic Patriarchs - sun bayyana cewa za su soke bukukuwanmu kirsimeti tare da takaita bukukuwa zuwa bukukuwan addini.

"Idan an yi la'akari da halin da ake ciki, musamman a Gaza, Patriarchs suna neman gafarar rashin karbar gaisuwar kirsimeti da na sabuwar shekara." Kamar yadda su ukun suka bayyana a cikin wani jawabi da suka yi na hadin gwiwa, inda ya bayyana cewa za su takaita bukukuwa zuwa "addu'o'i."

Ma'aikatar lafiya da ke yankin Falasdinawa da ke karkashin ikon Hamas ta bayyana cewa sama da mutane 20,000 suka rasa rayukansu a zirin Gaza tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare masu karfi ta sama da kasa a matsayin martani ga babban harin 7 ga watan Oktoba.

Mafiyawancin wadanda suka rasu mata ne da kananan yara, kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Harin Hamas ya kashe akalla mutane 1,140 a Isra'ila, mafiyawanci fararen hula kamar yadda kididdigar musamman ta AFP ta bayyana.

No comments

Powered by Blogger.