Header Ads

Hadakar sojojin Amurka ta samu cikas bayan Faransa, Sufaniya da Italiya sun fice daga cikin ta

Jirgin ruwa na yaki mallakin kasar Amurka, USS Bataan, na tafiya a cikin tekun Red Sea a ranar 8 ga watan Oktoba na shekarar 2023

A cikin wani babban cibaya ga hadakar sojojin ruwa karkashin jagorancin Amurka a tekun Red Sea domin samar da kariya ga jiragen ruwan Isra'ila da jiragen ruwan kasuwanci da suka shafi Isra'ilan ta samu, kasashen Faransa, Sufaniya da Italiya a hukumance sun dakatar da tarayyarsu a cikin hadakar.

Kamar yadda ya ke a cikin wani rahoton kafar watsa labarai ta Press TV, kasashen a fili sun bayyana niyyarsu ta yin aiki a karkashin umarnin manyan kungiyoyin kasa-da-kasa kamar majalisar dinkin duniya, NATO ko kungiyar tarayyar turai, tare da zabar kada su hade da Amurka.

Ma'aikatar tsaron kasar Faransa a cikin wani jawabi ta bayyana cewa tana goyon bayan samar da 'yancin tafiye-tafiye a tekun Red Sea da kuma wuraren da ke zagaye da ita, inda ta bayyana cewa tuni tana a yankin.

Sai dai ta bayyana cewa jiragen ta za su kasance karkashin umarnin Faransa kuma ba ta bayyana ko za ta karo sojojin ruwa ba.

Ma'aikatar tsaron kasar Italiya ta bayyana cewa za ta turo jiragi sojojin ruwa na Virginio Fasan zuwa tekun na Red Sea domin kare muradan kasar ta sakamakon neman hakan da wasu masu jirgin ruwa 'yan kasar Italiyan suka yi.

Ta bayyana cewa wannan na cikin Bangaren ayyukanta ne, kuma bai shafi hadakar sojojin ruwa da Amurka ke jagoranta ba a hanyoyin ruwan.

Bayan haka, ma'aikatar tsaron kasar Sufaniya ta bayyana cewa za ta yi aiki ne kawai a karkashin ayyukan da suka shafi NATO ko kuma wadanda suka shafi tarayyar turai.

"Ba za mu yi aiki a kashin kan mu ba a ayyukan tekun Red Sea." Kamar yadda ta bayyana.

A ranar Alhamis, Pentagon ta bayyana cewa sama da kasashe 20 sun yarda su yi aiki a karkashin jagorancin hadakar sojojin ruwan ta Amurka a tekun Red Sea, wadda aka sani da Operation Prosperity Guardian.

Rashin fayyace me kasashe za su runka yi ya haifar da rudani ga kamfanonin jiragen ruwa, inda wasu daga cikinsu suka runka canza hanya daga yankin, yayin da sojojin Yemen ke kai hare-hare da jirage marasa matuka da makamai masu linzami a tekun Red Sea a matsayin martani kan yakin Isra'ila a Gaza.

Shugaban ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta Pentagon, Lloyd Austin, ya bayyana kirkiro hadakar - wadda ta hada da Bahrain, Kanada, Faransa, Italiya, the Netherlands, Norway, Seychelles, Sufaniya da Ingila - a ranar Talata. 

A ranar Alhamis, Austin ya bayyana cewa Greece da Australia sun shiga kungiyar, inda suka zama 20, amma sai ya ce akalla kasashe takwas da ke ciki sun fice ba a bayyana su a fili ba.

 Mutanen kasar Yemen sun bayyana goyon bayansu ga yunkurin Falasdinawa ne tun bayan da kasar mamaya ta Isra'ila ta kaddamar da mummunan harin ta a ranar 7 ga watan Oktoba bayan da masu fafutika Falasdinawa suka kaddamar da harinsu na bazata wanda aka sawa suna Operation Al-Aqsa Storm, kan kasar 'yar mamaya.

Hare-haren Isra'ila ba kakkautawa kan Gaza ya yi sanadiyyar rasuwar mutane akalla 20,253, mafiyawancinsu mata da kananan yara, yayin da wasu mutanen 53,688 suka raunata.

Rahotanni sun nuna cewa kamfanonin jiragen ruwan Isra'ila tuni suka yanke shawarar canza hanyoyinsu domin tsoron hari daga sojojin Yemen.

Sojojin na Yemen sun ma kai hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka a yankunan da Isra'ila ta mamaye bayan yakin Isra'ilan a kan Gaza.

No comments

Powered by Blogger.