Header Ads

INEC ta yi wa daraktocin hukumar huɗu ritayar dole

Shugaban Hukumar zabe ta kasa, INEC.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tilasta wa daraktocin ta huɗu yin ritaya.

Shugaban Kwamitin Wayar da Kan Masu Jefa Ƙuri'a a hukumar, sannan Kwamishinan Tarayya, Mista Sam Olumekun, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

Yi masu ritayar dole ɗin ta biyo bayan fara aiki da sabuwar dokar da ta ƙayyade wa'adin shekaru takwas ga kowane daraktan da ke aiki ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya.

Olumekun ya ce, "Bisa aiki da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar a cikin wata sanarwa mai lamba HSCF/SPSO/268/T3/2/37, wadda aka fitar a ranar 27 ga Yuli, 2023, Hukumar Zaɓe ta bi wannan umarnin ta hanyar umartar dukkan daraktocin da su ka shafe shekaru takwas su na aiki a INEC, ko sama da haka, da su gaggauta yin ritaya.

"Bisa tsarin wannan umarni, daraktoci huɗu daga INEC za su ajiye aiki su tafi ritaya. Biyu daga cikin su Shugabannin Sassa ne a Hedikwatar INEC da ke Abuja, sauran biyu ɗin kuma Sakatarorin Tsare-tsaren Ayyuka ne a wasu ofisoshin hukumar da ke jihohi."

Sai dai kuma ya yi ƙarin hasken cewa wannan tsarin bai shafi manyan jami'an hukumar masu aiki a ɓangaren kula da lafiya ba, kamar yadda ita kan ta takarda mai lamba MH 7205/T31 ta nuna, wadda aka fitar a ranar 7 ga Satumba, 2023.

"Hukumar Zaɓe na yi wa daraktocin da sallamar ta shafa fatan alheri a rayuwar da za su ci gaba, bayan yin ritayar su," inji Mista Olumekun.

No comments

Powered by Blogger.