'Yan sanda a kasar Kenya sun gano gawarwaki 179 a wani daji da ke da alaka da wani malamin majami'a
'Yan sandan kasar Kenya a ranar Juma'a sun bayyana cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon al'amarin kungiyar Shakahola Kenya sun kai 179, mafi yawancinsu yara.
'Yan sandan sun yi imanin cewa gawarwakin da aka gano din a wani gari mai suna Malindi da ke gabar tekun Indiya, na mabiyan Paul Nthenge Mackenzie ne, wani direban motar tasi da ya koma mai wa'azi wanda ake zargin ya tunzurasu su ki cin abinci domin su mutu "su hadu da Jesus."
Wani kwamishinan yankin, Rhoda Onyancha, ya bayyana cewa ba wanda aka samu cetowa daga cikin babban dajin a ranar Juma'a.
Ruwa mai karfi ya hana binciken da ake yi da kuma aikin haka ramuka a satin da ya gabata, inda aka cigaba a ranar Talata.
Tuni dai mutane 25 - wadanda suka hada da Mackenzie da kuma wasu "masu tabbatar da yadda abubuwa ke tafiya" masu tabbatar da cewa ba wanda ya daina yin azuminsa ko ya bar dajin da ransa - suna hannun 'yan sanda kamar yadda Onyancha ya bayyana.
Ba a bar Mackenzie ya yi wani bayani ba amma wata kotu a ranar Laraba ta bayar da umarnin a tsare shi na wasu satuka uku kafin a karasa bincike a wani al'amari da yanzu da ake yiwa lakabi da "Kisan Kiyashin Dajin Shakahola."
'Yan sanda sun kama malamin majami'ar mai shekaru 50 wanda ya kirkiro majami'ar Good News International Church ne a ranar 14 ga watan Afirilu bayan 'yan sanda sun shiga cikin dajin Shakahola a karon farko.
A yayin da rashin cin abinci ke nuni cewa shine sanadiyyar mutuwar tasu, wasu daga cikin wadanda abin ya shafa -ciki har da yara- an duke su ne, an buge su ko an shake su kamar yadda wani shugaban masana ciwuwwukan jiki na gwamnati, Johansen Oduor, ya bayyana.
Takardun kotu a ranar Litinin sun bayyana cewa wasu gawarwakin an cire sassan jikinsu, inda 'yan sanda ke ikirarin cewa wadanda ake zargin na neman sassan jiki ne.
Sai dai ministan cikin gida, Kithure Kindiki, ya nemi da a kula, inda ya bayyanawa manema labaru a ranar Talata cewa, "Wani al'amari ne da muke binciken sa."
Wannan al'amari dai ya ba mutanen Kenya mamaki, wanda hakan ya sa shugaban kasar, William Ruto, kafa kwamitin bincike a cikin mace-macen tare da kafa wata kungiya wadda za ta yi duba da dokokin da ke kula da kungiyoyin addini.
Wani malamin majami'a da ake zargi na da alaka da Mackenzie da kuma gawarwakin da aka samu a cikin dajin an sake shi kan beli a yayin da ake sauraron shari'a a satin da ya gabata.
Post a Comment