Header Ads

Gwamnati na za ta mutunta 'yancin kafafen yaɗa labarai, za ta karɓi yabo, gyara da suka daga 'yan jarida da marubuta - Tinubu

Shugaba Tinubu tare da mawallafa jaridun

Shugaba Bola Tinubu ya ƙara jaddada cewa gwamnatin sa a ko yaushe za ta mutunta 'yancin kafafen yaɗa labarai da 'yan jarida, kuma za ta yi maraba hannu biyu da ra'ayoyin masu nuni da yin gyara, suka ko yabon gwamnatin sa.

Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce
Tinubu ya yi wannan bayani ranar Litinin, lokacin da ya gana da mambobin Ƙungiyar Mawallafa Jaridu ta Nijeriya (NPAN).

Shugaba Tinubu ya tabbatar masu da cewa zai zauna a tsanake ya duba buƙatar da suka bijiro masa da ita, wato ta neman a sassauta tsarin hada-hadar takardar buga jarida, wanda ke ci wa gidajen jaridu tuwo a ƙwarya ta hanyar tsadar takardun a cikin gida.

Da ya koma kan wahalhalun da matafiya ke fuskanta a yanzu lokacin tafiya hutun Kirsimeti da sabuwar shekara, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta ɗauki matakan sauƙaƙa tsadar zirga-zirga da sufurin jiragen sama, na ƙasa da kuma kan titinan motoci.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ne ya jagoranci tawagar masu gidajen jaridun a wannan ziyarar da suka kai wa Shugaba Tinubu.

Shugaban ya ci gaba da cewa ana nan ana ɗaukar matakan da za a rage farashin gas.

"Na damu sosai dangane da abin da ke faruwa a cikin ƙasar nan. Ina gode maku kan goyon bayan da ku ke bayarwa da ra'ayoyi da sukar da ake yi wa gwamnatin mu. Ba domin goyon bayan wasu daga cikin ku ba, ba zan zama shugaban ƙasa ba, har ga ni a yanzu tare da ku a matsayin shugaba.

"Kun jajirce kan aikin ku cikin rintsi da tsanani. Don haka mu kuma za mu ci gaba da mutunta ra'ayoyin ku, ko da kuwa ba mu yarda da abin da ku ka faɗa kan mu ba.

"Abu ɗaya da zan faɗa maku shi ne, ina karanta kowace jarida, ina kuma karanta ra'ayoyin da ake rubutawa, har ma da shafukan manazarta da marubuta ra'ayoyi daban-daban," inji Tinubu.

A jawabin sa, Ministan Yaɗa da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada kyakkyawar aniyar Gwamnatin Tarayya ta shata wa kafafen yaɗa labarai kyakkyawar shimfiɗa a ƙasar nan.

"Dimokraɗiyyar mu ta ginu ne a kan tsari da tafarkin ƙa'ida da tabbatar da komai bisa kyakkyawan tsarin doka da kuma 'yancin yaɗa labarai da bayanai.

"Rawar da kafafen yaɗa labarai musamman jaridu ke bayarwa ta na da tasiri da muhimmanci a wannan turbar dimokraɗiyya," cewar Minista Idris.

Daga nan Idris ya jinjina wa jagororin NPAN saboda samar da ƙungiya mai ƙarfin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa da kuma bayar da damar sauraren muryoyin jama'a mabambanta ra'ayoyi da fahimta.

Shi kuma Shugaban NPAN, kuma shugaban kamfanin Media Trust, masu buga Daily Trust, Trust TV da Aminiya, Malam Kabiru Yusuf, ya fara da yi wa Shugaba Tinubu murnar nasarar zaɓe da kuma nasara a Kotun Ƙoli. Daga nan ya ci gaba da lissafo matsalolin da suka dabaibaye masana'antu da hada-hadar takardar buga jaridu.

No comments

Powered by Blogger.