Header Ads

Kirkiro hadakar tsaron teku ta Amurka: Yemen ta ce za ta mai da tekun Red Sea "makabarta"

Ministan tsaron kasar Yemen, Mejo Janar Mohammad al-Atifi

Ministan tsaron kasar Yemen, Mejo Janar Mohammad al-Atifi, ya yi watsi da kirkirar hadakar tsaron teku karkashin jagorancin Amurka a tekun Red Sea, inda ya gargadi kawancen na kasashen yamma da cewa duk wani hari a kan kasar Yemen zai haifar da mummunan sakamako. 

"Mun mallaki makamai da soji da za su iya nutsar da jiragen ruwan ku na yaki, jiragen karkashin ruwa na yaki da jiragen ruwa masu dauke da jiragen sama na yaki (aircraft carriers)." Kamar yadda Mejo Janar Mohammad al-Atifi ya bayyana a ranar Litinin, inda ya kara da cewa, "Sojojin Yemen za su mayar da tekun Red Sea makabartar hadakar wadda Amurka ke jagoranta in har hadakar ta yanke shawarar daukar wani mataki a kan kasar Yemen." Kamar yadda ya bayyana yayin wani biki a birnin Sana'a.

Kamar yadda ya ke a cikin wani rahoton kafar watsa labarai ta Press TV, a dai ranar Litinin ne shugaban ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, Lloyd Austin, ya bayyana kirkiro hadakar tsaron teku karkashin jagorancin Amurka da ta hada da kasashen Bahrain, Kanada, Faransa, Italiya, Netherlands, Norway, Seychelles, Sufaniya da Ingila domin gudanar da sintiri a tekun na Red Sea a matsayin wani mataki kan hare-haren da Yemen ke kaiwa kan jiragen ruwan da suka nufi yankunan da Isra'ila ta mamaye, inda hare-haren na zuwa ne a matsayin martani sakamakon yakin da gwamnatin da ke Tel Aviv ta ke yi a zirin Gaza. 

Mutanen Yemen dai sun bayyana goyon bayan su ne a fili ga yunkurin Falasdinawa tun bayan da Isra'ilan ta kaddamar da mummunan yaki a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba. 

Hare-haren Isra'ila ba kakkautawa a Gaza sun yi sanadiyyar rasuwar mutane 19,453, mafiyawancinsu mata da kananan yara, a Gaza, inda wasu 52,286 suka samu raunuka.

Kamar yadda kafar ta bayyana, tuni dai jiragen ruwan Isra'ila suka canza hanyoyin da suke bi domin tsoron hare-hare daga sojojin kasar Yemen.

Har wa yau, sojojin na kasar Yemen sun kai hare-hare da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka a wurare da ke yankunan da Isra'ila ta mamaye biyo bayan yakin na Isra'ila a Gaza.

No comments

Powered by Blogger.