Header Ads

INEC za ta gudanar da zaɓuɓɓukan da kotu ta soke da na cike gurabu 34 cikin Fabrairu 2024 - Yakubu

Shugaban Hukumar zaɓe ta kasa, Farfasa Mahmood Yakubu 

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa mai yiwuwa a satin farko na Fabrairu, 2024 za ta gudanar da ragowar zaɓuɓɓukan da za a sake da kuma na cike gurabun a wasu mazaɓu, yankuna da shiyyoyin tarayya da jihohi.

Shugaban hukumar, Farfasa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a taron da INEC ta yi da jam'iyyu ranar Litinin, a Abuja.

Yakubu ya ce INEC ta ɗaura aniyar gudanar da zaɓuɓɓukan biyu, wato zaɓukan da za a sake da kuma waɗanda ba a samu gudanarwa ba duk a rana ɗaya. Wato ya na nufin har da zaɓukan cike gurabu kenan.

Ya ƙara da cewa yayin da aka kafa Kotunan Sauraren Ƙararrakin Zaɓe bayan kammala zaɓen 2023, to yanzu dai za a ce sun kusa kammala zaman su.

"Abin da ya rage shi ne hukumar zaɓe ta gudanar da zaɓuɓɓukan da kotuna suka bada umarnin a sake a wuraren da za a sake zaɓuɓɓukan.

Yakubu ya ce INEC za ta kuma gudanar da zaɓuɓɓukan cike gurabun waɗanda suka mutu, ko waɗanda suka ajiye muƙaman da aka zaɓe su a kai a Majalisar Ƙasa ko Majalisar Jihohi.

"Kamar yadda ku ka sani, shi zaɓe na 're-run', zaɓe ne da ya ƙunshi jam'iyyu da 'yan takara waɗanda suka rigaya suka fafata a babban zaɓe. Sai fa idan jam'iyya na buƙatar musanya ɗan takara idan ya rasu kafin a sake wannan zaɓen da za a yi.

"Shi kuma 'bye-election', zaɓe ne sabo da za a yi. Don haka a wannan tsari, tilas ne jam'iyyu su sake gudanar da zaɓen fidda gwanaye cikin ƙa'idar kwanakin da dokar zaɓe ta gindaya.

"Zuwa yanzu dai Kotunan Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe sun umarci INEC ta gudanar da zaɓuɓɓuka a mazaɓu 34 da suka ƙunshi shiyyar sanata ɗaya, sai mazaɓun ɗan majalisar tarayya guda 11 da majalisun jihohi 22.

"Sai dai kuma daga zaɓuɓɓuka 34 ɗin da za a sake, guda wurare uku ne kawai za a sake zaɓen baki ɗaya."

A ƙarshe Yakubu ya ce sai bayan an kammala sauraren shari'un zaɓen gwamnoni a kotunan tarayya da Kotun Ƙoli, sannan hukumar sa za ta tattara yawan shari'un da aka gudanar, domin yin bayanin su dalla-dalla.

No comments

Powered by Blogger.