Sai na zama shugaban kasar nan; in ba yau ba, to zai kasance lokaci mai zuwa - Peter Obi
Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bayyana cewa ba ya bata lokacin sa kuma sai ya zama shugaban kasar Nijeriya.
Obi ya bayyana haka ne a yayin da ya ke kaddamar da wani littafi mai suna: "Peter Obi: Many Voices, One Perspective." a Awka, babban birnin jihar Anambra a ranar Juma'a.
Peter Obi dai ya zo na uku ne da yawan kuri'u a zaben shugaban kasar shekarar 2023 da ya gabata. Kaddamar da littafin an shirya shi ne domin samar da kudi ga Obi din domin dan takarar shugaban kasar ya iya cigaba da shari'ar zaben a kotu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
"Duk wanda ke tunanin zan tafi ne yana bata lokacin sa ne. Bari in fada maku, sai na zama shugaban kasar nan. Ina da tabbacin hakan. Idan ba yau ba ne, dole ya kasance gobe ne."
"Sauran mutanen da suke so su zama, su zo su fada mana me suke so su yi, kuma ya za su yi. Wannan kasa ta ce, bana da shaidar zama dan kasa daban-daban guda biyu. Idan wani na tunanin zan gudu daga Nijeriya, to bai yi gaskiya ba.
"Ina da abubuwa guda uku da zan yi a Legas da kuma Anambra a yau. Zan yi jawabi a Legas a daren yau. Ba za mu gudu daga Nijeriya ba. Ba na zaku da in zama shugaban kasa ba ne, amma na san sai ya faru.
"Shekaru na uku ina a kotu a Anambra domin in karbi matsayina na gwamna, in kalubalanci al'amarin. Mutane da yawa sun yi kokarin rage min kwarin gwiwa, amma sai na ce ko da duka shekaru hudun za su kare domin mu tabbatar da al'amarin mu yi gyara ga yadda abubuwa ke tafiya, zai tabbata.
"Na halarci wani taro a jiya a Abuja, taron hukumar abinci ne ta duniya. Na saurari wani rahoto da ya ce Nijeriya za ta fuskanci yunwa a shekara mai zuwa.
"Nijeriya ce za ta fuskanci yunwa ba Peter Obi ba. Rahoton ya lissafo jihohin Borno, Yobe da Adamawa a matsayin inda al'amarin zai yi kamari, amma wadannan jihohin in an hada su duka sun fi fadin kasar Isra'ila, Misra na fitar da abinci amma Nijeriya ba ta iya ciyar da kan ta.
"Dole mu koyi dabi'ar yin abinda ya dace, idan ba mu yin abinda ya dace watarana mu abubuwa za su shafa baki daya.
"Sai na zama shugaban kasar nan; in ba yau ba to karo mai zuwa. Ba ina cikin rudani ba ne ko; ba wai ina gaggawa ba ne. Na sadaukar ne kan hanyar samar da kyakkyawar Nijeriya." Kamar yadda ya bayyana.
Dan takarar shugaban kasar ya ma bayyana cewa zai mutunta hukuncin kotu a cikin sabanin da ake samu kan zabe.
"Muna cikin zaman lafiya, ba za mu yi rigima da wani dan siyasa ba. Kada ku rasa kwarin gwiwa saboda rokon yafiyar jama'a da na yi. A matsayinmu na matasa, ba za mu yi fada da iyayenmu ba, ko da muna da gaskiya."
Post a Comment