Header Ads

Iran za ta karbi rukunin farko na jiragen yaƙin SU-35 daga Rasha

Samfurin jitagen yaki SU-35 kenan

Kasar Iran za ta karbi rukunin farko na jiragen yakin SU-35 daga kasar Iran a cikin sati mai zuwa, kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Kasar Iran da Rasha na kara karfafa dangantakar da ke tsakaninsu a yayin da kasashen yamma ke tsaka da sa takunkumi ga kasar. Kasar ta Iran da Rasha sun sa hannu a cikin wata babbar yarjejeniya a 'yan watannin da suka gabata domin bunkasa tattalin arzuki, safarar kayayyaki, makamashi da hadakar soji.

Kafar watsa labarin kasar Iran da ke amfani da yaren Fasha ne ta fito da labarin, inda kuma ba ta yi bayani cikakke dangane da jigilar ta su ta jirgin ruwa ba. Jiragen yakin na SU-35 jirage ne na zamani wadanda aka tsara domin gudanar da manyan ayyuka a sararin samaniya.

A cikin watannin da suka gabata, akwai labarai a kafafen watsa labaru da ke magana kan amsar jiragen yakin da Iran za ta yi daga kasar Rasha.

Wakilin Iran na din-din-din a majalisar dinkin duniya a cikin watan Maci ya tabbatar da cewa kasar Iran ta kammala yarjejeniyar karbar jiragen. Kafafen watsa labarun Iran a lokacin sun bayyana cewa jiragen guda 24 ne za a kawo kasar Iran.

Shahriar Heideri, wani mamba a kwamitin tsaron kasa da siyasar kasashen waje na majalisar kasar Iran, ya bayyanawa kafar watsa labaru ta Tasnim news agency a cikin watan Janairu cewa jiragen yakin za su zo ne a cikin wannan shekarar ta kalandar Iran wadda ke farawa daga ranar 21 ga watan Maci.

Heideri ya ma bayyana cewa kasar ta Iran za ta karbi na'u'rorin tsaron sararin samaniya, na'urorin makami mai linzami da jirage masu saukar angulu (Helicopters) daga kasar ta Rasha nan gaba kadan.

Kasar Iran ba ta sayi wasu sababbin jiragen yaki ba a cikin shekarun da suka gabata, in ban da jiragen yakin MiG-29 Fulcrum da ta saya kadan a 1990s.

Bayan MiG-29, hukumar sojojin sama ta Iran (IRIAF) na amfani ne da jiragen yakin da aka gyara a gida na F-4 Phantom II, F-14 Tomcat da kuma F5-E/F Tiger II daga 1970s wadanda gwamnatin Pahlavi da ke samun goyon bayan Amurka ta karba kafin juyin-juya halin musulunci a shekarar 1979.

No comments

Powered by Blogger.