Header Ads

Malaman aikin jinya 'yan Nijeriya sama da 75,000 suka koma kasashen waje cikin shekaru biyar

An bayyana cewa malaman jinya da masu aikin unguwar zoma da ba su gaza 75,000 ba suka bar kasar nan sakamakon rashin albashi mai kyau, rashin wurin aiki mai kyau da sauransu a cikin shekaru biyar.

Shugaban kungiyar ma'aikatan jinya da aikin unguwar zoma ta Nijeriya (NANNM), Kwamared Michael Nnachi, ya bayyana haka yayin taron satin ma'aikatan jinya na kasa-da-kasa da aka yiwa lakabi da "Our Nurses, Our Future"

Rashin tsaro da ke addabar kasarnan, musamman sace mambobin su domin neman kudin fansa da kuma fada da mambobin su a yayin da suke yin aikinsu kamar yadda doka ta tanada, an bayyana cewa suna cikin dalilai, kamar yadda NANNM ta bayyanawa kafar watsa labarun The Nation.

"Sakamakon rashin albashi mai kyau da kuma wurin aiki mai kyau, ma'aikatan jinya da masu aikin unguwar zoma sama da 75,000 suka bar Nijeriya a cikin shekaru biyar.

"Karancin ma'aikatan jinya da masu aikin unguwar zoma a wasu bangarorin kwarewa da kuma yankunan kasa, raguwar karfin aiki da kuma rashin isassun ma'aikatan jinya ya sa ma'aikatan jiniyar na yin aiki mai yawa ba tare da samun karin biya saboda haka ba, wannan na kara sawa su fuskanci hadurra tare da rage samar da ingantaccen aikin kula da lafiya."

Mataimakin shugaban kungiyar ta NANNM, Israel Blessing, a bangarensa ya bayyana cewa, "Rahoton shekarar 2021 na State of the World's Midwifery ya bayyana cewa ana da karancin unguwar zoma 30,000 a Nijeriya wanda ke nufin kashi 6 a cikin 100 a cikin mutane 10,000. Domin cike wannan gibi zuwa shekarar 2030, ana bukatar ma'aikatan jinya kimanin 70,000, to amma a yadda kiyashin yanzu ya nuna, 40,000 ne kawai za a iya samu zuwa shekarar 2030. Wannan karancin ya fi yawa ne a arewacin Nijeriya inda ake bukatar wadanda za su kula da bangaren mata masu ciki da bangaren abinda ya shafi haihuwa."

A yayin da ya ke nasa jawabin, babban sakatare janar/ rijistira na kungiyar ma'aikatan jinya da masu aikin unguwar zoma a Nijeriya, Mista Faruk Abubakar, ya bayyana aikin jinya a matsayin babban aiki a duka fadin duniya kuma wani abu kebantacce mafi girma a duniya, inda ya bayyana cewa, "Domin samun Universal Health Coverage (UHC) ( samun ingantaccen kula da lafiya a duniya baki daya) ciki har da Nijeriya, dole kasar ta samar da ma'aikatan jinya da suka dace a kuma wajen da ya dace, a lokacin da ya dace tare kuma da ilimin da ya dace domin samar da aikin lafiya domin goben mutanenmu."

No comments

Powered by Blogger.