Header Ads

Saudiyya za ta tura mace ta farko 'yar kasar zuwa sararin samaniya a cikin shekarar 2023

'Yan sama jannatin Saudiyya

Saudi Arabiya ta bayyana cewa za ta tura mace ta farko 'yar asalin Saudiyya, Rayyanah Barnawi, da namiji dan Saudiyya, Ali Al-Qarni, zuwa tashar sararin samaniya ta kasa-da-kasa a cikin watanni shida na farko na shekarar 2023 kamar yadda rahoton Saudi Press Agency ya nuna.

Bayan Rayyanah Barnawi da kuma namiji daya mai ilimin sararin samaniya shima, Ali Al-Qarni, da za su tafi tashar sararin samaniya a cikin watanni shida na farko a wannan shekara, akwai ma wasu masanan ilimin na sararin samaniya, Mariam Fardous da Ali Al Gamdi, su kuma wadanda za a yi masu horo a kan cimma bukatu daban-daban wadanda suka shafi sararin samaniya. 

Za su tafi ne tare da tawagar AX-2 zuwa tashar sararin samaniyar, kamar yadda hukumar sararin samaniyar ta bayyana a shafin ta na Twitter.

"Manufar wannan shine kara karfin da kasa ke da shi a bangaren sararin samaniya domin samar da cigaba ga daukacin bil-adama ta hanyar samar da damammaki da ke tare da masana'antar sararin samaniya, tare da yin taimako a bangaren bincike da ya shafi bangarori da dama kamar lafiya, dorewar yanayin muhalli da kuma fasahar sararin samaniya." Kamar yadda Saudi Press Agency ta bayyana.

Wannan tafiya sararin samaniya wadda daga kasar Amurka aka shirya masana sararin samaniyar za su tashi, hadaka ce ta kungiyoyi da dama wadanda Ma'aikar Tsaro, Ma'aikatar Wasanni, Hukumar Jiragen Sama, Asibitin Kwararru da Cibiyar Bincike na Sarki Fahad da sauran mataimaka daga kasashen duniya da suka hada da Axiom Space, wadanda suka kware bangaren tafiye-tafiye sararin samaniya da kuma samar da kayayyakin sararin samaniya a kasar Amurka ke jagoranta.

No comments

Powered by Blogger.