An saki wani mutum bayan an yi kuskuren daure shi har tsawon shekaru 28 a Amurka
An saki wani mutum dan kasar Amurka mai suna Lamar Johnson a Missouri da ke Amurka bayan an yi kuskuren daure shi a kurkuku tsawon shekaru 28.
Lamar Johnson dai ana zarginsa ne da laifin kisan kai wanda ya sha musantawa, to saidai a ranar Talata, wani alkali mai suna David Mason da ke kotun St. Louis ya yanke hukuncin da ya wanke mutumin.
Alkalin ya ce ya yanke hukuncin ne bayan wasu shaidu biyu sun gabatar da wasu gamsassun hujjoji da ya yarda da su da kuma suka nuna Lamar Johnson, wanda ke da shekaru 50, ba shi da laifi.
A dai shekarar 1994 ne aka yanke masa hukunci bayan da aka zarge shi da laifin kashe wani mutum mai suna Marcus Boyd, kuma Lamar Johnson ya sha nanata cewa baya gida a lokacin da aka far wa Marcus Boyd tare da kashe shi.
Wasu mutane biyu ne dai da fuskokinsu a rufe suka kashe Marcus Boyd a gaban gidan Lamar Johnson a cikin watan Oktobar shekarar 1994.
Alkali Mason ya yanke hukunci ne bayan da wani shaida ya soki bahasin da ya bayar, inda wani fursuna ya fadi gaskiyar shi tare da wani mutum mai suna Phil Campbell ne suka harbe Boyd.
Magoya bayan Lamar Johnson dai sun yi ta sowa da kuma murna da tafi lokacin da kotu ta sanar cewa ta wanke shi.
Post a Comment