Kudan zuma ya kashe karamin yaro daya da jikkata mutane da dama a Garu-Illela
A safiyar yau Laraba, a sakamakon tashin kudan zuma a unguwar Canchawa da ke garin Garu, wani yaro ya rasa ransa da wata akuya, yayinda mahaifiyar yaron da ya rasu da yayyen yaron da wata tsohuwa da lamarin ya rutsa da su duk suna asibiti suna karbar magani.
Kudan zuman dai ya kai shekaru 20 a cikin gidan da wannan al'amari ya faru, kawai yau sai ya fara bore har ta kaiga rasa rai da raunata wasu.
Wasu jajartattun matasa ne suka sami damar tsaida kudan zuman ta hanyar cigaba da kunna wuta a muhallin da abin ya faru.
Allah ya kiyaye gaba, ya kuma jikan wanda ya rasa ransa.
Post a Comment