Header Ads

Minista Na So 'Yan Kasuwa Su Zuba Jari Don Haɓaka Shirin Iskar Gas Na CNG

 Daga hagu: Abokin haɗin gwiwa, Mohammed El-Gawish; Minista Alhaji Mohammed Idris, da Ciyaman na ABG Group, Alhaji Bawa Garba, a wurin ƙaddamar da masana'antar ABG CNG Plant tare da yaye injiniyoyin CNG su 40 a ranar Talata a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga 'yan kasuwa da su kasance kan gaba a shirin nan na Gwamnatin Tarayya na yin amfani da Matsattsiyar Iskar Gas (CNG) a ƙasar nan.
 
Hadimin Musamman kan Yaɗa Labarai na ministan, Malam Rabi'u Ibrahim, ya faɗa a cikin wata sanarwa ga manema labarai cewa ministan ya furta haka ne a ranar Talata a Abuja a wurin ƙaddamar da masana'antar iskar gas ta ABG CNG tare da yaye injiniyoyin 40 da su ka ƙware a harkar sarrafa CNG ɗin. 
 
Idris ya ce wannan ƙoƙari da rukunin kamfanonin ABG Group ya yi abu ne wanda ya dace kuma ya zo a kan kari.

Haka kuma ya ce amfani da matsattsiyar iskar gas wani abu ne wanda ya zo kenan kuma shi ne hanyar rage kashe kuɗi a ɓangaren harkar sufuri.

Idris ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan yadda ya jagoranci yadda za a koma ana amfani da iskar gas ta CNG a maimakon man fetur a motocin haya da ƙanana na shiga. 
 
Ya ce: “Iskar gas ta CNG ita ce za a riƙa amfani da ita nan gaba, don haka ya na da muhimmanci ga 'yan kasuwa a Nijeriya su yi amfani da wannan damar ta shirin gwamnati kan CNG ɗin ta hanyar zuba jari na ɗaukar ma'aikata da sayen kayan aiki da ake buƙata don haɓaka sashen a duk faɗin Nijeriya."
 
Ministan ya bayyana cewa ya zuwa yanzu har gwamnatin Tinubu ta kasafta naira biliyan 100 a matakin farko ga harkar gas ɗin CNG, kuma ma har ga shi Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi na'am da shirin CNG ɗin wanda hakan ya taimaka wajen sanyin da ta yi kan maganar da ke tsakanin ta da Gwamnatin Tarayya.
 
Shugaban rukunin kamfanonin ABG Group, Alhaji Bawa Garba, a nasa jawabin, ya ce amfani da iskar gas ta CNG wani maganin matsala ne salin alin wanda ya ke buƙatar goyon baya da ciniki daga gwamnati idan har ana so ya faɗaɗa har a riƙa yi wa Nijeriya kallon “Ƙasar Iskar Gas.”
 
Ya ce: “Kamfanin mu ya na godiya ga Shugaba Tinubu saboda bajintar da ya yi wajen yanke shawarar a riƙa yin amfani da CNG. Mu da ma can kamfani ne wanda ke fara yin abu, don haka shaidar shigar mu cikin tsarin CNG ita ce yadda mu ka horas da ɗimbin injiniyoyin sauya CNG a faɗin Nijeriya.”
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris (a tsakiya) a wajen ƙaddamar da masana'antar ABG CNG Plant da yaye injiniyoyin CNG guda 40 a ranar Talata a Abuja

No comments

Powered by Blogger.