Header Ads

Kashi 69 cikin 100 na 'yan kurkuku a Nijeriya na jiran shari'a, 3,413 an yanke masu hukuncin kisa

Hukumar gyaran dabi'u ta Nijeriya (NCS) ta bayyana cewa kashi 69 na 'yan kurkuku da ta take da su su 77,894 a fadin kasa ke jiran a yi masu shari'a yayin da 3,413 aka yanke masu hukuncin kisa.

Kakakin hukumar, Malam Abubakar Umar ne ya bayyana haka ga 'yan jarida a ranar Juma'a, inda ya kara da cewa hukumar na da 'yan kurkuku 77,894 maza 76,081 mata 1,768 a tare da ita "ya zuwa ranar Litinin 18 ga watan Disamba."

Kamar yadda yadda ya ke a cikin wani rahoton kafar watsa labarai ta PM News, 53,836 da suka hada da maza 52,512 da mata 1,324 na jiran a yi masu shari'a a cewar kakakin.

"Wadanda ke jira a yi masu shari'a (ATP) wadanda ke tare da mu sune kashi 69 cikin 100 na gabadaya mutanen da ke cikin kurkukun. Wannan babbar matsala ce a garemu." Kamar yadda ya bayyana, inda ya ce hukumar na aiki domin tabbatar da cewa ana yi shari'a ba tare da bata lokaci ba.

Kakakin ya bayyana cewa sakamakon taimako daga ministan cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, hukumar ta samu damar rage yawan wadanda ke tsare a gidajen kurkuku.

"Tsarin ministan ya tabbatar da sakin 'yan kurkuku 4,086 wadanda ke da zabin biyan tara ko diyya." Kamar yadda yadda shaida.

Malam Umar ya ce wannan shekarar ta shaida cigaba dangane da kulawa ga 'yan kurkukun, musamman dawo da yanayi mai kyau a garesu, gyara dabi'unsu da komawarsu cikin jama'a, inda ya bayyana cewa 'yan kurkuku 1,840 sun yi jarabawar NECO/SSCE a shekarar 2023 yayin da kuma da dama ke yin karatuttuka daban-daban a gidajen kurkuku da ke fadin kasar.

No comments

Powered by Blogger.