Header Ads

A biya ASUU albashinsu na watanni takwas da aka rike - NUT ga gwamnatin tarayya

Kungiyar malamai ta Nijeriya (NUT) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da, ba tare da bata lokaci ba, ta biya mambobin kungiyar malaman jami'a (ASUU) albashinsu na tsawon watanni takwas da aka rike yayin da suka gudanar da yajin aikin da ya gabata.

Kungiyar ta ma nemi gwamnati a kowanne mataki da ta daina nuna halin ko in kula ga bangaren ilimi daga matakin firamare zuwa manyan makarantu.

Babban sakataren kungiyar ta NUT, Dakta Mike Ene, ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da ya yi da kafar watsa labarai ta the Nigerian Tribune.

Kamar yadda ya bayyana, gwamnatin tarayya bai kamata ta cigaba da dabi'a kamar mambobin na ASUU sun farka ne kawai sun tafi yajin aiki ba a lokacin da suka tafi, kawai saboda ba su da wani zabi ne domin a biya masu bukatunsu.

Ya nemi gwamnatin tarayya da ka da ta sanya wani sharadi wajen sakin albashin malaman jami'ar, inda ya yi ikirarin cewa tsarin "kin biya domin ba a yi aiki ba" ba a san da shi ba a tsarin ma'aikata a fadin duniya, saboda haka Nijeriya ba za ta zama daban ba.

Daktan a yayin da ya ke kira ga duka gwamnatocin jihohin da malaman firamare da na sakandare ke bin kudi su biya su kafin karshen shekarar 2023, ya bayyana cewa "malamai ya kamata su yi rayuwa mai kyau."

Kamar yadda ya bayyana, kayayyaki sun yi tsada ta yadda iyalai da dama ba sa iya sayen su a kasa, kuma malamai wadanda albashinsu dama bai taka kara ya karya ba bai kamata ana rike shi ba kuma.

Ya bayyana cewa abin damuwa ne a ce gwamnati na gaggawar shiga yarjejeniya ta kuma sanya hannu a yarjejeniyar bayan ta san ba za ta mutunta yarjejeniyar ba.

Ya bayyana cewa irin dabi'un gwamnati da 'yan siyasa zai cigaba da haifar da rashin cigaba ga kasa.

Ya bayyana cewa sashen ilimi na bukatar kulawa matuka da kudi daga gwamnati a kowanne mataki, kuma duk abinda ya shafi sashen, zai shafi sauran bangarorin tattalin arzukin kasa.

"Shi ya sa muke kira ga gwamnati a kowanne mataki da su tashi su yi abinda ya hau kan su su samar da kudade ga ilimi a shekara mai zuwa." 

Ene ya kara da cewa sama da malamai 6,000 a makarantun gwamnati za su yi ritaya a karshen shekara, amma gwamnati ta na kokarin ta maye gurbin guda 1,000 ne kawai a cikinsu. 

Ya bayyana cewa gwamnati bai kamata ta jira a fara fuskantar matsaloli sakamakon rashin isassun malamai a makarantun gwamnati ba kafin ta fara daukar matakan da ya dace domin maye gurbinsu.

No comments

Powered by Blogger.