Header Ads

Mutane sama da 570,000 a Gaza suna cikin "yunwa" sakamakon yaki: Rahoton majalisar dinkin duniya

Wasu fararen hula a Gaza

A wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta saki a ranar Alhamis ya gano cewa sama da mutane rabin miliyan na cikin "yunwa" a Gaza saboda rashin isasshen abinci da ke shiga yankin tun bayan da yaki ya barke satuka 10 da suka gabata.

"Yanayi ne da kusan kowa a Gaza na jin yunwa." Kamar yadda babban masanin tattalin arzuki na shirin abinci ta duniya (World Food Program), Arif Husain, ya bayyana.

Ya yi gargadin cewa in har yaki a tsakanin Hamas da Isra'ila ya cigaba a wannan matakin kuma ba a daidaita shigo da abinci ba mutanen na iya fuskantar "cikakkiyar yunwa a cikin watanni shida masu zuwa." 

Kamar yadda kafar watsa labarai Arab News ta ruwaito, rahoton, wanda aka saki a ranar Alhamis kuma wanda hukumomin majalisar dinkin duniya da kungiyoyin da ba na gwamnati ba 23 suka saki ya gano cewa gabadaya mutanen Gaza suna cikin bukatar abinci, inda mutane 576,600 ke cikin matsananciyar bukata, ko kuma matakin yunwa.   

Ma'aikatan jinkai na majalisar dinkin duniya a ranar Alhamis sun kawo rahoton yanayi "matsananci" a asibitoci biyu a arewacin Gaza inda marasa lafiya da ke kan gado wadanda ba a yi maganin ciwukan su ba ke kukan a ba su ruwa, likitoci da ma'aikatan jinya 'yan kadan da suka rage ba su da sauran kayan aiki, kuma an jera mutane a wajen asibiti - alamomi da ke yin nuni da kara tsanantar al'amurra bayan satuka 10 na yaki a tsakanin Hamas da Isra'ila.

Ma'aikatan jinkai sun yi magana ne kwana daya bayan sun kai kayayyaki a asibitocin Ahli da Shifa wadanda ke a tsakiyar yankin da ake yaki na arewacin Gaza inda sojojin Isra'ila suka rusa mafiyawan birnin yayin yaki da Hamas.

Isra'ila ta bayyana cewa ta na a mataki na karshe na kakkabe Hamas daga arewacin Gaza amma watannin yaki na gaba a kudancin Gaza. Yakin wanda aka fara shi bayan mummunar kutsawar Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma kama mutane a Isra'ila ya haifar da rasuwarsa Falasdinawa kusan 20,000. Wasu mazauna Gaza mutane miliyan 1.9 - sama da kashi 80 cikin 100 na mutanen yankin - sun bar muhallansu.

No comments

Powered by Blogger.