Header Ads

An wanke Ba'amurke daga laifin kisa bayan ya yi shekaru 48 a kurkuku

Glynn Simmons sanye da kayan kurkuku

Wani mutum daga jihar Oklahoma da ke Amurka, Glynn Simmons, wanda aka zarga da laifin kisa a wani shagon sayar da barasa yayin wani fashi da aka yi a shekarar 1975 kotu ta wanke shi daga wannan laifi a ranar Talata bayan ya yi shekaru sama da 48 a cikin kurkuku.

Simmons, wanda ke da shekaru 70 a yanzu an zarge shi ne da aikata laifin kisan lokacin da ya ke dan shekaru 22, kuma Alkali Amy Palumbo na kotun yankin Oklahoma ne ya yanke hukuncin ba ya da laifi, kamar yadda NY Times ta ruwaito. 

Kamar yadda kafar ya ke a wani rahoton kafar watsa labarai ta Sahara Reporters, wani umarni wanda aka gyara mai dauke da sa hannun Alkali Palumbo a ranar Talata ya bayyana cewa kotu ta gano "ta hanyar hujjoji da suke a fili masu gamsarwa" cewa laifin da ya sa aka sa Simmons cikin kurkuku "ba Simmons ne ya aikata ba."

Kamar yadda sashen wanke laifuffuka ya bayyana, Simmons ya kwashe lokaci mai yawa a kurkuku - shekaru 48 da wata daya da kwana 18 - fiye da duk wani da aka wanke shi daga tuhumarsa.

Kamar yadda sashen wanke laifuffuka na kasar Amurka, wanda shi ne ke bin diddikin lokutan da aka kwashe a kurkuku sakamakon hukuncin da ba daidai ya ke ba, ana tunanin wannan shine lokaci mafi tsawo da wani ya kasance a kurkuku bayan an yanke mai hukunci ba tare da ya aikata laifi ba a Amurka.

"Wannan wani darasi ne a kan dagewa." Simmons ya bayyana dangane da shari'arsa yayin wani taron 'yan jaridu bayan an yanke hukuncin, "Ka da wani ya fada maku ba zai iya faruwa ba, saboda tabbas zai iya faruwa." 

Joe Norwood, wanda ya ke shi ne lauyan Simmons, ya bayyana cewa hukuncin wanda aka yanke a ranar Talata ya ba Simmons damar samun diyya har ta dalar Amurka 175,000 kuma ta ba shi damar shigar da karar gwamnatin kasa.

Nowood ya bayyana cewa Simmons, wanda a yanzu haka an bincika yana da kansa, na rayuwa ne ta hanyar taimakon da ake yi masa ta hanyar wata kafa a yanar gizo.

No comments

Powered by Blogger.