Header Ads

Ma'ajiyar banki ta bai daya: Kotu ta ce a dawo da dala miliyan 793.2 da aka boye a bankuna bakwai

Mizani, Alamar kotu

Wata babbar kotu a jihar Legas ta bayar da umarni ga bankunan kasuwanci har guda bakwai a Nijeriya da su dawo da kudi har dalar Amurka 793,200,000 da aka yi ikirarin an boye su ba bisa ka'ida ba wanda hakan karya kundun tsarin ma'ajiyar kudi bai daya ne (TSA) na gwamnatin tarayya.

Alkali mai yanke hukunci, Chuka Obiazor, a ranar Alhamis ya bayar da umarni ga bankunan da su dawo da kudaden ga bangaren kudaden dala da aka gano na babban bankin Nijeriya (CBN) wanda ya ke daban-daban da aka ajiye a wurinsu ba kan ka'ida ba.


Umarnin an bayar da shi ne bayan kotu ta saurari karar da mataimakin Antoni Janar na kasa, Farfesa Yemi Akinseye-George, ya shigar.

Yayin da ya ke kare karar, Farfesa Yemi Akinseye-George, ya bayyana cewa zai fi dacewa da muradin adalci na kotu da ta bayar da umarni ga bankunan da su dawo da kudaden ga gwamnatin tarayya domin gujewa karkatar da su, sa su inda bai dace ba, sace su ko kuma yin amfani da su yadda bai dace ba.

 Ya ma bayyana cewa kudaden da aka ruke gwamnati ta bukace su domin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2017.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels ta ruwaito, bayan sauraronsa sai Alkalin ya bayar da umarnin.

Ya ma bayar da umarnin a wallafa wannan umarni a jaridun da ke fitowa kullum.

A farkon watan Agustar 2015, gwamnatin tarayya ta bayar da umarni ga duka ma'aikatu da hukumomi (MDAs) da su rika sa kudaden su a ma'ajiyar bankin ta bai daya (TSA).

Gwamnatin na kyautata zaton cewa umarnin zai taimaka wajen gudanar da al'amurra ba tare da boye-boye ba tare da bin dokokin da ke sashe na 80 da 162 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.

Tsarin ya shafi babban bankin Nijeriya (CBN), kamfanin man fetur na kasa (NNPC), hukumar tashoshin ruwa ta kasa (NPA) da kuma hukumar kula da harkokin jiragen ruwa (NIMASA) da dai sauran ma'aikatu da hukumomi da dama.

No comments

Powered by Blogger.