Header Ads

Malaysia ta haramta wa jiragen ruwan Isra'ila zuwa ƙasar


A ranar Laraba, Malaysia ta haramtawa duk wani jiragin ruwan Isra'ila ko wanda ya shafi Isra'ila zuwa tashoshin jiragen ruwan ta yayin da hankali ke cigaba da tashi sakamakon hauhawar mace-macen Falasdinawa a Gaza.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Arab News ta ruwaito, ma'aikatan lafiya a zirin Gaza sun bayyana cewa hare-haren sama da ake yi a kullum sun kashe mutane kusan 20,000 - mafiyawancinsu mata da kananan yara.

Haramta zuwan jiragen ruwan Isra'ila na kamfanin jiragen ruwan ZIM da Malaysia ta yi ba tare da bata lokaci ba da kuma duk wani jirgin ruwa da ke dauke da tutar Isra'ila, sanarwa ce wadda Firaministan kasar ta Malaysia, Anwar Ibrahim, ya yi.

"Wadannan takunkuman sakamako ne na irin ayyukan da Isra'ila ke yi da ba su mutunta ka'idojin jin kai tare da keta dokokin kasa-da-kasa tare da cigaba da yin kisan kiyashi da tursasawa ga Falasdinawa." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

"Malaysia ta ma sa takunkumi ga duk wani jirgi da zai tafi Isra'ila wanda zai yi lodi a tashoshin ruwan Malaysia. Wadannan takunkuman a take sun fara aiki."

Kamar yadda ya ke a rahoton Arab News, Anwar ya bayyana cewa gwamnati ta kyale jiragen ruwan ZIM da su yada zango a Malaysia daga shakarar 2002 zuwa sama.

Kamfanin jiragen ruwa na ZIM dai shine kamfanin jiragen ruwa da ke daukar kwantaina na 10 mafi girma a duniya, kamar yadda kundin yanar gizo mai samar da bayanan sirri kan jiragen ruwa na Alphaliner ya bayyana.

Malaysia ba ta da wata cikakkiyar alaka da Isra'ila a hukumance a yayin da ta kasance mai magana sosai wajen nuna goyon bayan ta ga 'yancin Falasdinawa.

Ta ki barin 'yan kasarta su yi amfani da fasfo dinsu domin zuwa Isra'ila sannan ta ki barin 'yan Isra'ila zuwa kasar.

Collins Chong Yew Keat, wani masanin siyasar kasashen waje da tsaro daga "University of Malaysia" ya bayyana cewa haramtawar na zuwa ne sakamakon tsayawa kyam kan tsaurarawa ta Malaysia a kan Isra'ila.

Tursasawa daga kasashen duniya na kara hauhawa a kan yakin kuma "akwai karin hauhawar yin Allah wadai kan dabi'un Isra'ila." Kamar yadda ya bayyanawa Arab News.

"Haramtawar a kan jiragen Isra'ila wani mataki ne da aka yi zaton sa wanda aka yi a matsayin wani sako na nuna matsayar Malaysia a kan al'amarin."

No comments

Powered by Blogger.