Header Ads

'Yan bindiga sun sace Alkaliya da kashe dan sanda mai taimaka mata a Akwa Ibom

Wasu 'yan bindiga 

'Yan bindiga sun sace wata alkaliyar babbar kotu, Joy Uwana, a jihar Akwa Ibom da ke kudu-maso-kudun Nijeriya.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Premium Times ta ruwaito, an dai sace Alkaliyar ne a ranar Litinin a kan babban titin karamar hukumar Oron da ke jihar, inda kuma 'yan bindigan suka harbe dan sandan da ke taimaka ma ta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom, Odiko MacDon, ya tabbatar da faruwar al'amarin kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito.

Alkaliyar an sace ta ne yayin da ta ke kan hanyar ta ta zuwa gida a Uyo bayan zaman kotu a Oron.

"Wannan al'amari ne na bakin ciki." Kamar yadda Channels TV ta ruwaito MacDon na fada a kan al'amarin.

MacDon ya bayyana cewa kwamishinan 'yan sandan jihar ta Akwa Ibom, Olatoye Durusinmi, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin al'amarin.

"A yanzu haka da muke magana, ba inda ba za a bincika ba, za a samar da kudade domin tabbatar da cewa an dawo da Alkaliyar ga iyalanta a kowanne lokaci daga yanzu. 

"Na yi magana da iyalan jami'in da aka kashe, wanda kafin rasuwarsa ya kasance mai taimakawa ne ga Alkaliyar. Za a yi adalci kuma wadanda suka aikata wannan abu za su shigo hannu." Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana.

Sace mutane domin neman kudin fansa yanzu ya zama daya daga cikin manyan laifuffuka a biranen Nijeriya. 

'Yan siyasa, 'yan kasuwa da duk wani da ya ke mai abin hannunsa, ciki har da yara 'yan makaranta, ba su tsira ba.

No comments

Powered by Blogger.