Header Ads

Harkar musulunci a Nijeriya ta yi kira ga shugaban Amurka da ya dakatar da kisa a Gaza

Shugaba Biden na Amurka

Harkar musulunci karkashin Shaikh Zakzaky, wadanda aka fi sani da 'yan Shi'a, sun yi kira ga gwamnatin Amurka wadda shugaba Biden ke jagoranta da sauran shugabannin kasashen duniya da su goyi bayan tsagaita wuta ba tare da bata lokaci ba a hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza wanda ke cigaba da faruwa a Palastinu.

Kamar yadda yake a cikin wani rahoton kafar watsa labarai ta Sahara Reporters, Harkar Musuluncin ta yi kiran ne a cikin wani jawabi da ta fitar a ranar wata Talata daga Shaikh Sidi Mainasara, inda ta bukaci Joe Biden da ya dakatar da duk goyon bayansa ga Isra'ila domin a tsayar da kashe "mata da yaran Gaza wadanda ba su dauke da makami."

"Tun ranar 7 ga watan Oktobar 2023 Isra'ila ta cigaba da hare-haren ta a kan mutanen Falasdinu, mafi yawanci mata da yara, lalata gine-gine da kai hari asibitoci. Mun ga bidiyoyin mutane suna kuka saboda azabtarwa, kananan yara suna zaune a cikin jini a kan rusassun gine-gine, mahaifa dauke da 'ya 'yansu da suka rasu.

"Wannan na kona zuciyarmu da ruhunanmu tare da haifar mana da radadi wanda ba za mu iya jure mawa ba. Ga shi ana kama mutane a arewacin Gaza, da kai harin bom ba bisa ka'ida ba, katse hanyoyin sadarwa, lalata duka asibitoci, inda duk sun daina aiki.

"Hare-hare na cigaba da faruwa kuma kasar mamaya ta Isra'ila na cigaba da yin kisan kiyashi kan mutanen Falasdinawa, maza, mata, yara duka da cikakken goyon bayan Amurka.

"Saboda la'akari da haka, muna kira ga Amurka da ta tsayar da kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza ba tare da bata lokaci ba."

A baya dai Isra'ila ta kafe cewa sai ta share kungiyar Hamas bayan harin ta na ranar 7 ga watan Oktoba.

A dai ranar 7 ga watan Oktoba ne zaman dar-dar a tsakanin kungiyar da Isra'ila ya kai makura inda kungiyar ta kaddamar da harin da ba ta taba yi ba a baya a kan Isra'ila.

Kungiyar ta kama mutane 240. Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar hare-hare ta sama wadanda suka kashe mutane sama da 19,000 a Gaza.

No comments

Powered by Blogger.