Header Ads

Shugabannin duniya, masana, sun yi Allah wadai da "kisan kiyashin" Isra'ila a Gaza

Hayaki ya tashi sama biyo bayan hare-haren sama na Isra'ila a birnin Gaza a ranar 12 ga watan Oktobar shekarar 2023.

Akalla shugabannin duniya 155, masana da malamai suka sa hannu a wata takarda domin yin Allah wadai da "kisan kiyashin" da sojojin Isra'ila suka kwashe wata daya suna yi a kan Falasdinawa da ke zirin Gaza da aka zagaye.

Takardar ta bayyana cewa Isra'ila ta cigaba da aikata laifuffukan ta tare da kin sauraren kiraye-kirayen da ake yi da zanga-zanga a duniya na a samar da dawwamammiyar tsagaita wuta.

"A wannan halin da ake ciki wannan takardar ba wai kawai tana kira ne da yin Allah wadai ba amma domin a dauki dawwamammen mataki domin hana faruwar haka." Kamar yadda takardar ta hadin gwiwar ta bayyana.

"Mun hadu domin gaggawar bukatar hakan a yanzu, wanda ya sa dole masanan duniya su hadu su nuna rashin goyon bayansu ga wannan mummunan al'amari da ya samu mutanen Falasdinu, bayan haka, a dauki mataki ga wadanda suke da iko, domin hakan nauyi ne a yi."

"A yanzu haka, mace-mace na kara karuwa, tsarin kula da lafiya a Gaza ba zai iya kulawa da wadanda suka jikkata ba, barazanar yunwa da yaduwar cututtuka na kara karuwa a kullum." Kamar yadda jawabin ya bayyana. 

"Sake kaddamar da yakin soji akan fararen hular Gaza na nufin rashin mutunta shugabancin majalisar dinkin duniya, dokoki da mutuntaka, gaba daya, da kuma kima ta mutum." Kamar yadda wani sashe na takardar ta bayyana..

Kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na kafar watsa labarai ta Press TV, wadanda suka sa hannu a takardar sun hada da tsohon Firaministan Turkiyya, Ahmed Davutoglu, Javad Zarif, tsohon ministan harkokin kasashen wajen Iran; Amr Moussa, tsohon babban sakataren majalisar kasashen larabawa; Chris Hedges, tsohon shugaban jaridar The New York Times a gabas ta tsakiya da sauran su da dama.

A Gaza, kusan mutane 19,500 suka rasu sakamakon hare-haren Isra'ila, sai dai a wata ziyara da ya kai a yankunan da Isra'ila ta mamaye a ranar Litinin, sakataren tsaron kasar Amurka, Lloyd Austin, ya jaddada cikakken goyon bayan Washington ga Tel Aviv tare da yin alkawarin samarwa kasar karin makamai. 

Lloyd ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da manyan jami'an Isra'ila wadanda suka hada da Firaminista Benjamin Netanyahu da kuma ministan yakin kasar, Yoav Gallant.

No comments

Powered by Blogger.