Header Ads

Nijeriya na rasa dala biliyan 7 duk shekara sakamakon rashin gudanarwa mai kyau a tashoshin jiragen ruwa

Majalisar wakilan Nijeriya

'Yan majalisar wakilai biyu, Hon. Julius Ihonvbare da Hon. Ibrahim A. Isiaka, suka bayyana haka a cikin wani kuduri na hadaka da suka gabatar bayan dawowar zaman majalisar a ranar Talata.

Kamar yadda suka bayyana, Nijeriya na karbar kashi 10 cikin 100 ne na kayayyakin da ake shigowa da su yammacin Afirka a maimakon kashi 60 cikin 100 da aka ware ga Nijeriya, sauran kuma kasashe makwafta ne ke samu.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Vanguard ta ruwaito, 'yan majalisun sun bayyana cewa akwai bukatar majalisar ta gudanar da cikakken bincike domin gano damarmaki da Nijeriya ke rasawa a duk shekara.

Sakamakon haka, majalisar ta yanke shawarar dora nauyi a kan kwamitocin ta na tashoshin jiragen ruwa, tsara tattalin arzuki, ilimin harkokin da suka shafi jiragen ruwa da kuma kwamitin masu harkokin jiragen ruwa na Nijeriya da su yi cikakken bincike a kan alfanun tashoshin jiragen ruwa da sauran abubuwan da suka shafi tattalin arzuki na ruwa.

Yayin da ya ke gabatar da kudurin, Hon. Ihonvbare ya bayyana cewa sashen jiragen ruwa na Nijeriya na da matukar muhimmanci wajen dorewar tattalin arzukin Nijeriya, inda ya koka a kan tashoshin jiragen ruwan wadanda ba su samun cikakkar kulawa da cewa za su iya kara habaka yanayin kudin shigar kasar.

Ihonvbare ya bayyana cewa, "Tashoshin jiragen ruwan Nijeriya da kyar suke samun kashi 10 cikin 100 na kayayyakin da ake shigowa da su kasashen yammacin Afirka a cikin kashi 60 cikin 100 da ya kamata su zo Nijeriya, wanda babban rashi ne ga tattalin arzuki sakamakon rashin kulawa mai kyau, inda aka kiyasta hakan da dalar Amurka biliyan 7 a duk shekara. 

"Mafi yawancin jiragen ruwa da ke kawo kayayyaki Nijeriya sun fi son su je wasu tashoshin ruwan ba na Nijeriya ba. Tabbas kasar jamhuriyar Benin na amfana da babbar kasuwar Nijeriya, a yayin da Kwatano ta kasance wata matattara ta shigowa da kayayyaki;

"... Jiragen ruwa da ke dakon kaya da dama ana rasa su ga kasar Togo da sauran kasashe makwafta inda suke sauke kayayyakin da ake sake sawa a jiragen ruwa domin kawowa Nijeriya sakamakon rashin mahada ta jiragen ruwa mai kyau." Sai ya bayyana sauran wasu matsalolin da suka shafi tashoshin jiragen ruwan wadanda suke haifar da rasa kudade na jiragen ruwan, "Da aka kiyasta da naira biliyan 250 a shekarar 2016 kadai."

Ya koka a kan yadda Nijeriya ta kasa samar da isassun kayayyaki domin rage wahalhalu ga tashar jirgin ruwa ta Legas da kuma dalilin da ya sa tashoshin jiragen ruwan Kalaba, Fatakwal, Warri da Koko ba za a iya sawa su cigaba su kasance wata mahada ta shigowa da kayayyaki a yankin ba.

No comments

Powered by Blogger.