Header Ads

'Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da sace wasu 6 a jihar Sokoto

Wasu mutane rike da bindiga

Wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne a ranar Talata sun afka kauyen Tursa da ke karamar hukumar Rabah da ke jihar Sokoto inda suka kashe mutum daya tare da sace wasu mutane shida.

Kamar yadda yadda ya ke a cikin wani rahoton kafar watsa labarai ta PM News, jaridar The Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar al'amarin a daren ranar Talata.

Rufai ya bayyanawa Punch cewa, "'Yan bindigan sun shiga kauyen ne inda suka sa wuta a wani daki tare da kona mutum daya da ya ke ciki.

"Sun ma kona mashina guda biyu yayin afkuwar wannan al'amari tare da sace mutane shida inda shanu wadanda ba a san iyakar su ba aka sace su yayin faruwar al'amarin."

Sai dai ya bayyana cewa kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayar da umarnin binciko wadanda ake zargi da aikata laifin.

No comments

Powered by Blogger.