Header Ads

Kisan Sani Rai's: Tawagar Shek Zakzaky ta Mika ta'aziyar sa ga Iyaln Mmarigayin




Daga Hussaini Ibrahim



Shehin Malamin Addini Musulimci a na Nageriya, Jagoran Harkar Musulumci Shaikh Ibrahim Yakuba Al Zakzaky (h) ya tura Tawagar wakilansa,karkashi jagorancin Malam Nafiu, domin yin ta'aziyya gami da jajantawa ga iyalan marigayi Malam Sani Ra'is Funtuwa.da 'yan bindiga su kayiwa kisan gilla a Gidan sa da ke Funtuwa.


Wakilan Shek Zakzaky,Malam Nafiu, sami ganawa da Iyaye da iyalai da 'yan uwan marigayi Malam Sani Ra'is, inda suka isar da sakon Jagora (H ) na ta'aziyyar kisan gillar da a kayi mi shi,  gami da jajantawa akan 'ya'yan Marigayin guda biyu (2) da 'yan ta'addan su ka tafi da su.



Da yake amsar gaisuwar,Kanin Mahaifiyar Malam Sani Rais, Malam Labiru Funtuwa,ya nuna matukar farin cikin su da ganin wannan tawaga mai albarka.kuma ya mika sakon godiya ga Shek Zakzaky da kuma sanya Iyalan Marigayi cikin addua dan kubutar da su daga hannan  'Yan bindiga.


Daga karshe wakilan sunyi Addu'a ga marigayin tare da fatan Allah (SWT) Ya gaggauta kubutar da 'ya'yan marigayin daga hannun 'yan ta'addan.


Adaren Juma'a ne  9/9/2022, 'Yan bindigan su kaiwa Gidan Sani Muhammad Lawal Rais, marubuci kuma manomi dirarmikiya a Gidan sa da ke  Sabuwar Abuja cikin Karamar hukumar Funtuwa jihar Katsina , 'yan bindigan sun nemi sutafi da shi Daji shi kuma yaki tafiya yayi iya kokarinsa wajan ganin ya turjemasu wannan ne ya sanya suka fito da shi bayan gida sa suka bude masa wuta suka kashe shi anan take .


Kisan Sani Rai's Funtuwa da 'Yan bindiga su kayi ya girgiza al'umma matuka mu samman masu bibiyar Rubutun sa da ya keyi na fagen Ilimin sanin Taurari da hisabi. da kuma kokarin bayyana ma Al'umma wanene Imamul Hujja (AJ).


Al'umar Musulmi da Kiristoci  da makwabtansa zukatan su sun bugu a lokacain da suka samu labarin cewa, 'Yan bindigan sun kashe Sani Rais , sabo da yadda suke amfani da Rubutun sa da kuma tallafi da ya ke basu da kyakkyawar mu'amalar sa da su.


Marigayi Sami Rais ya Kware wajan hada lisafin aka harufan Al'kurani da wayar wa mutane wasu lamuran da ake shiga dimuwa acikin su. Misali kamar su ,sanin suwaye ,Ai'mma a cikin Litafin Baibul wanda Kiristoci ke amfani da shi tsohonsa da sabon sa ,sai kuma rubutunsa na baya bayanan na sabuwar shekara ta Musulumci ta 1444,yayi Rubutun akan hijira ta 14444,har mukara ta 14.a cikin wannan satin , sai kuma rubutunsa na karshen wanda ya saki kafafen sada zumunta wanda ana gobe ne 'Yan bindiga zasu kashe shi watau ranar Laraba Mai taken "MAKOMAR RAUNANA DA AKE ZALUNTA' . Daga Litafin Imamul Mahadi (A) da labarin gaibu "daga silasalr bayani Sayyid Hassan Nasarullah. Daga shafin na 40 zuwa 46.


Wannan Rubutu na marigayi Sani Rais shine na karshe wanda ya saki dan karuwar al'umma. 


Marigayi Sani Rais Mutum ne mai neman nakansa halak wannan ya sanya ya maida hankali wajan Noman Damuna da na Rani da kiwo, duk da baiwar da Allah yayi masa ta Kimiya fasaha wajan hada FM tasa alokacin da ya zamo zakara wajan gyaran Redio da Talabijin.


Marigayi Sani Rais Allah ya amshi ransa ne sakamakon kisan 'Yan bindiga Yana dashekaru 53 aduniya  ya bar mata daya da 'ya'ya shadaya. kuma babban Dansa Yayi Shahada ne alokacin Waki'r Zariya inda Sojoji suka kashe shi a Gyalesu Gidan Sayyid Zakzaky (H) .


kuma yanzu haka abunda takaici 'Yan bindiga suntafi da yaran sa biyu , Mace 'yar shekara 15,da namijin Dan Shekara Tara.

No comments

Powered by Blogger.