Header Ads

Shin ya dace gwamnati ta yi wa jama'a karin kudin waya?

Jama'a da dama da Almizan ta tambaye su, ko ya dace a kara kudin amfani da layukan waya a kasar nan? Sai jama'a suka rika kukan, to da wanne za su ji in hakan ya auku?

Rahotanni sun tabbatar da cewa za a kara wa ‘yan Najeriya kudin amfani da waya nan da wani dan lokaci, bayan da gwamnatin kasar ke shirin sanya wani sabon haraji kan kamfanonin sadarwa.

Hakan ya biyo bayan bayanin da Ministar Kudi da Kasafi da kuma Tsare-tsaren Kasa Zainab Ahmed, ta yi ne cewa gwamnatin tarayya za ta dora wa kamfanonin sadarwa biyan harajin kwastan na kashi biyar cikin dari.

Ministar ta yi bayanin ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da tsarin harajin kwastan din jiya Alhamis a Abuja, wanda hukumar sadarwa ta kasar (NCC) ta shirya.

Kasancewar daman tuni masu amfani da waya suna biyan kashi 7.5 cikin dari na harajin kayan alatu (VAT), a yanzu wannan harajin na kwastan na kashi 5 cikin darin ma zai hau kan masu amfani da wayar ne.

Nauyn zai hau kan masu amfani da waya ne kamar yadda shugaban kungiyar masu kamfanonin sadarwa a Najeriyar (Association of Licensed Telecom Owners of Nigeria (ALTON)), Gbenga Adebayo ya sanar.

Mista Gbenga ya ce, kasancewar ba za su iya saukaka kudin amfani da waya da sauran hanyoyin sadarwar ba wannan ne ya sa dole su karkatar da nauyin ga jama’a.

Ya ce, za su yi hakan ne saboda ‘’Tuni daman suna biyan haraji-haraji har 39, ga kuma matsalar wuta da suke fama da ita inda suke kashe makudan kudade wajen sayen man gas na dizil.''

No comments

Powered by Blogger.