Header Ads

'Yan bindiga sun hallaka 'yan sa kai mutum 41 a jihar Katsina

'Yan bindiga sun hallaka 'yan sa-kai mutum 41 a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina bayan wata arangama da ta faru a tsakaninsu a karamar hukumar.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SB Gambo Isah, ya shaidawa 'yan jaridu a yammacin ranar Juma'a a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ya bayyana cewa 'yan bindiga dauke da muggan makamai da bindigogi kirar AK 47 sun dira a gidan wani mutum mai suna Alhaji Muntari da ke zaune a garin Unguwar Audu Gare, Kandarawa a cikin karamar hukumar Bakori inda suka kashe dabbobi 30 tare da tafiya da shanu 50 cikin daji.

Bayan samun labarin ne sai 'yan sa kai suka shirya wata tawaga ta garuruwa 11 domin tunkarar barayin dajin su kwato dabbobi da shanun da suka sace kamar yadda sanarwar ta bayyana.

To saidai bayan da 'yan sakan suka bi barayin cikin wani daji mai suna Yargoje, barayin sun yi masu kwanton bauna, inda barayin suka kashe 'yan sakan har mutum 41 tare da raunata mutum biyu.

Bayan wannan al'amari da ya faru mataimakin 'yan sanda na shiyyar Malumfashi ya jagoranci zuwa inda lamarin ya afku domin daukar 'yan sakan su 41 da wadanda suka jikkata daga bisani kuma aka kai su babban asibitin Kankara.

Sanarwar daga karshe ta bayyana cewa an tura gamayyar jami'an tsaro domin kamo wadanda suka yi wannan ta'asa su fuskanci hukunci, kuma ana cigaba da gudanar da bincike.

No comments

Powered by Blogger.