Header Ads

Ministan Yaɗa Labarai ya bayyana ayyukan da Shugaban Ƙasa ya wajabta masa ya yi

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ɗora masa nauyin jaddada tasirin kishin ƙasa, aiki da gaskiya da kuma kawar da nuƙu-nuƙu, a matsayin kyawawan ɗabi'un da gwamnatin sa za ta ɗore kan turbar su.

Ministan ya bayyana haka a cikin tattaunawar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a Abuja.

Ya ce ajandar Fata Nagari Lamiri da Shugaba Tinubu ta hau mulki da ita, wani kyakkyawan muradi ne na ɗaukaka Nijeriya zuwa ƙololuwar nasara da bunƙasa a cikin manyan ƙasashe na duniya, tare da shafe baƙin fentin da ake kallo a jikin wannan ƙasar.

Idris ya ce Tinubu ya hore ni da na cewa na tabbatar mun samu nasarar wayar da kan 'yan Nijeriya cikin shekaru kaɗan masu zuwa, ta yadda aƙalla za mu iya sake kankaro ƙima da martabar ƙasar nan, tare da fara ɗorawa bisa kyakkyawar turbar da ta fi dacewa mu bi.

"Wannan kuwa babban kalubale ne. Saboda kun dai san ba a zukatan matasa kaɗai ɗa'a da kishi su ka yi ƙaranci ba, har ma a zukatan yara da manya.

"Ina ganin dalili kenan shugaban ya canja wa sunan Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Bunƙasa Al'adu, zuwa Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.

"Hakan kenan ya na nufin shugaban ƙasa na so ɗora batun wayar da kai da cusa kishin ƙasa a sahun gaba," cewar Idris.

Ministan ya ƙara da cewa tasirin kishin ƙasa da aiki da gaskiya da Tinubu ke ta faɗi-tashin cusawa da kwaɗaitarwa.

"Ya ba mu umarnin kai-tsaye cewa mu tabbatar waɗannan kyawawan ɗabi'u da halaye nagari sun kasance jigo a ƙoƙarin faɗakar da akasarin 'yan Nijeriya."

No comments

Powered by Blogger.