Header Ads

Halin da Najeriya je ciki a mulkin Buhari, nafila ne kan na 2015 Cewar tsohon Sarki Sunusi

Halin da Najeriya je ciki a mulkin Buhari, nafila ne kan na 2015 
Cewar tsohon Sarki Sunusi

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi Lamido na biyu ya bayyana damuwa kan halin da Najeriya ke ciki, yana mai cewa, kasar ta tabarbare fiye da yadda take a shekarar 2015, lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki daga hannun Goodluck Jonathan.

Sunusi na magana ne a wurin wani taro da Gidauniyar Akinjide Adeosun ta shirya kan sha’anin shugabanci a birnin Lagos da ke kudancin kasar a ranar Alhamis 04/08/22.

"Wannan ita kadai ce kasar da ke samar da man fetur amma take kokawa a halin yanzu, bayan da farashin man ya tashi sakamakon rikicin Rasha da Ukraine. Daukacin kudaden shigarmu ba za su iya biyan basukanmu ba," In ji Sunusi

Tsohon Sarkin na Kano ya kuma yi gargadin cewa, abin da aka gani a 2015 nafila ne kan abin da zai faru a 2023. Yana mai cewa, a halin yanzu Najeriya na fama da matsaloli da dama da suka hada da ta’addanci, hare-haren ‘yan bindiga da tsadar rayuwa da rashin tabbas kan farashin kudaden ketare.

Sunusi ya kuma diga ayar tambaya, yana mai cewa, ta yaya ne tarihi zai tuna shugaban kasa da gwamnoni da ministoci da suka shafe tsawon shekaru 8 kan karagar mulki?

No comments

Powered by Blogger.