Header Ads

Masana tattalin arzikin duniya sun ce wa Biden ya sakar wa Afghanistan kuɗinta da Amurka ta riƙe


Biden

Gwamman mashahuran masana tattalin arziki na Amurka da ma duniya ne suka bukaci shugaban Amurka Joe Biden ya sakar wa babban bankin Afghanistan kuɗi dala biliyan bakwai daga cikin kuɗaɗenta da Amurkar ta riƙe.

Masanan sun kuma buƙaci ƙasashen Birtaniya, da Jamus, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da su ma su saki wasu ƙarin biliyan biyu da su ma suka riƙe da su.

A wata takarda da suka rubuta, sun yi watsi da tayin da Amurkar ta yi na sakin rabin kuɗaɗen.

Sun kafa hujja da cewar kuɗaɗen mallakin Afghanistan ne halak-malak, kuma a yanzu ƙasar na matukar bukatar su kasancewar kashi 70 cikin 100 na al'ummar ƙasar ba su iya biyan hatta ƙananan buƙatunsu na wajibi.

Amurka da wasu ƙasashen duniya ne dai suka riƙe ƙuɗaɗen ƙasar ta Afghanistan bayan da Taliban ta karɓe ikon ƙasar a bara.

No comments

Powered by Blogger.