Header Ads

Ya za ka ji in kana cikin jirgin da barci ya kwashe matukinsa?

Matuka jirgin saman Ehiopia sun yi sabi-zarce bayan barci ya kwashe su

Jirgin saman Ehiopia
Image caption: Jirgin saman Ehiopia

Wasu matuka jirgin saman kamfanin Ehiopian Airlines biyu sun yi sabi-zarce har zuwa koluluwar da aka daina jin duriyar su bayan barci ya kwashe su.

Rahotanni sun ce masu kula da jiragen sama a filin jirgin saman da ke Habasha sun yi ta kokarin kiransu a waya to amma ina sun ringa sun kai kololuwar da ba za a iya samun su ba.

Bayan da kararrawar jirgi ta tashe su, sai suka yi kokari suka sauka a yunkuri na biyu.

Jirgin dai ya tashi ne daga filin jirgin saman Khartoum a Sudan.

Jirgin samfurin Boeing 737, mai daukar fasinjoji 154, na shafe kasa da sa'oi biyu ne idan zai je kasashe makwabta.

Mutane da dama ne dai suka bayyana mabambantan ra'ayoyi a kan barcin matuka jirgin a yayin aiki in da wasu suka tausaya musu tare da cewa aiki ne ke musu yawa shi ya sa barci ya kwashe su, wasu kuma sun mayar da abin raha har suna wallafa wa a shafukansu na tiwita cewa barci a yayin aiki ya kai matuka jirgi kuloluwa.

Masu sharhi kan al'amuran da suka shafi zirga-zirgar jirage sun bayyana matukar damuwarsu kan afkuwar lamarin a shafukansu na tiwita.

Ba a dai ji ta bakin kamfanin jirgin ba har yanzu.

No comments

Powered by Blogger.