Mutum ɗaya ya bace wasu 50 sun raunata bayan da wani gini ya kama da wuta, bangarensa ya tarwatse a Paris
Zuwa ranar Alhamis, ba a san inda mutum daya ya ke ba bayan da bangaren wani gini ya tarwatse a Paris, yayin da wasu mutum shida suke cikin mawuyacin hali tare da samun kulawa a asibiti a yayin da masu aikin ceto ke daga bangarorin ginin.
'Yan sanda sun bayyana cewa kimanin mutane 50 ne suka jikkata sakamakon tarwatsewa da rushewar ginin da ke kan titin Rue Saint Jacques, wanda ake tunanin fitar iskar gas ce ta haifar da shi.
"A cikin mutane biyu da ake nema a cikin rusasshen ginin, daya daga ciki an tafi da shi asibiti." Kamar yadda ofishin 'yan sandan ya bayyana, "Neman dayan kuma na cigaba." Kamar yadda suka kara da bayyanawa, inda suka yi gargadin cewa, "Wadannan alkaluman za su iya canzawa."
Tarwatsewar dai ta faru ne a ranar Laraba da yamma a yanki na biyar na birnin da ke kusa da Luxembourg Gardens a karshen Latin Quarter, wani muhimman wurin 'yan yawan bude ido da ke babban birnin na Faransa.
"Ya kasance abu mai matukar firgitarwa, na dauka girgizar kasa ce. Kowanne wuri yana motsawa." Violeta Garesteaw, wata mai kula da gida a kusa da ginin ta fadawa kafar watsa labaru ta AFP bayan share gilasai a kusa da yankin. "Winduna da dama sun fashe. Dole muka sa roba saboda ana ruwan sama." Kamar yadda ta bayyana. Girgizar ta shafi winduna da ke da nisan mita 400 (440 yards) daga wurin.
Wannan ya haifar da barkewar wuta wadda ta sa ginin- wanda ke dauke da wata makaranta ta kwalliya Paris American Academy- rushewa. Kamar yadda mahaifiyar daya daga cikin daluban ta rubuta a kafar sada zumunta ta Facebook ta makarantar, azuzuwan ba kowa ciki domin daluban sun tafi wajen Paris Fashion Show Week. "Da mutanen da abin ya shafa sai ya fi haka." Mataimakin magajin garin Paris, Emmanuel Gregoire, ya bayyanawa gidan rediyon FranceInfo.
An dai yi amfani da injinan wuta 70 kuma masu kashe gobara 270 suka yi aiki kafin a samu a iya kashe wutar.
A ranar Alhamis an rage yawan jami'an tsaro da aka sa a wurin domin barin 'yan jaridu da sauran 'yan kallo su matsa kusa da baraguzan ginin da ke kusa da asibitin Val-de-Grace.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Arab News ta ruwaito, a cikin watan Janairun 2019, wani fayep din iskar gas da ake zargin iskar na fita daga cikinsa ta yi sanadiyyar rushewar wani gini a Rue de Trevise da ke yanki na tara, inda mutane hudu suka rasa rayukansu ciki har da masu kashe gobara biyu. Girgizar ta fasa winduna masu yawa yayin da aka kwashe iyalai da dama wadanda har yanzu ba su dawo ba sakamakon aikin gyara da ake yi. Mafi yawan titin ba a bin sa shekara hudu kenan sakamakon mummunan al'amarin. Kuma gardama da ake ta fuskar doka dangane da dalilin fashewar ta cinye miliyoyin Euro na diyya ga wadanda abin ya shafa.
Post a Comment