Header Ads

Ranar Damisar Larabawa ta Duniya da Majalisar dinkin duniya ta ware abin farin ciki ne ga Saudiyya - Mai kula da dabbobi


Lokacin da majalisar dinkin duniya ta yi zabe a kan wani kuduri domin tabbatar da ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin Ranar Damisar Larabawa ta Duniya, shugaban kungiyar Panthera, wata kungiya da ke kokarin kiyaye magunan daji a duniya kuma shugaban kungiyar "Global Alliance for Wild Cat", Thomas S. Kaplan, ba karamar murna ya yi ba.

Damisar sananniyar abu ce a shekaru dubunnai a Saudi Arabiya, inda ake iya ganin zane-zanenta a jikin tsofaffin katangun Al-Ula, wani tsohon birni da ke yankin Madinah a arewa-maso-yammacin Saudi Arabiya, wanda ke yin nuni da muhimmancin damisar ga mutanen Saudiyya da kakanninsu, kamar yadda Kaplan ya bayyana.

Yanzu kuma samun muhimmancin Damisar ta Larabawa a babban taron majalisar dinkin duniya, "Wani babban abin farin ciki ne ga mutanen Saudiyya da masarautar kan ta." Kamar yadda mai kula da dabbobin ya bayyanawa kafar watsa labaru ta Arab News.

A cikin shekarar 2019, Kaplan ya sa hannu a wata yarjejeniya da ministan al'adu na Saudiyya kuma gwamnan hukumar masarautar Saudiyya da ke kula da Al-Ula, Yarima Badr bin Abdullah, domin taimakon ayyukan kula da dabbobi a yankin da kuma duniya, inda aka ba ayyukan kula da Damisar ta Laraba muhimmanci sosai domin samar da kariya ga dabbar da ke neman karewa a duniya wadda ta fito daga birnin na Al-Ula.

"Damisar Larabawa ita ce dabbar da ta fi fuskantar kalubale a cikin duka manyan maguna." Kaplan ya bayyana, "Saboda haka samun kwararriya kamar Saudiyya na taimaka mana a aikin da muke son yi tabbas wata kyauta ce daga Allah." Kamar yadda ya bayyana.

Kudurin na majalisar dinkin duniya da ya ware Ranar Damisar Larabawa ta Duniya "Nasara ce a fili, ga Damisar da masarautar." Ya kara da cewa.

"A wuraren da mu ke zuwa domin mu tseratar da damisa ko sauran dabbobi da ke a matsayin wani bangare na yawan bude ido a wani karamin yanki, mu kan je tare da mu da kara samar da kulawa da lafiya, gina makarantu, gina kananan asibitoci, (muna nunawa) mutanen kauyen cewa ba wai kawai ba abinda za su ji wa tsoro bane amma za ma su karu ta hanyar hayayyafar maguna, kuma cewa saboda damisa 'ya 'yansu za su samu damarmakin da suka shafi rayukansu da tattalin arzikin su." Kamar yadda ya bayyanaw a cikin bayanan da ya yi.

Magunan daji suna taka muhimmiyar rawa a yanayin muhalli. Ana daukar su a matsayin "nau'in halittu masu lema" yayin da ake daukar matakan da suka shafi kare dabbobi, saboda kokarin kare su kokarin kare sauran halittu ne ba kai tsaye ba. Hayayyafar magunan dajin kan iya taimakawa wajen tsirar baki daya muhallin su.

Har mutane ma za su amfana in dabbobin sun hayayyafa, domin za su kara karfafa yawan bude ido su kuma haskaka al'ummun kauyuka. Ga Saudi Arabiya, irin wadannan al'ummun za su iya zama wani muhimmin bangare na samar da cigaban masarautar, hakan kuwa zai sa kauyakun su samu kayayyakin more rayuwa da sauran damarmaki.

No comments

Powered by Blogger.