Header Ads

Zuwa yanzu kimanin alhazai miliyan 1.5 suka isa kasar Saudiyya

Kusan alhazai miliyan 1.5 suka isa Saudiyya daga kasashen waje tun bayan shigowar lokacin aikin Hajj kamar yadda Saudi Press Agency ta ruwato a ranar Alhamis.

A cikin alhazai 1,499,472 da suka je masarautar, 1,435,014 sun zo ne ta jiragen sama, 59,744 ta kasa sai kuma 4,714 ta ruwa.

A cikin wadanda suka zo ta jiragen sama, alhazai 230,170 sun amfana daga shirin hanyoyi na Makkah.

Kudin aikin Hajj na wadanda ke zuwa daga wata kasa ya ragu da kashi 39, kamar yadda ministan aikin Hajj da Umrah, Tawfiq Al-Rabiah, ya bayyana a ranar Alhamis.

Ya ma bayyana cewa yawan alhazan da za su yi aikin Hajj a wannan shekarar zai dawo kamar yawan wadanda ke yi kafin barkewar annoba (ta Coronavirus), kamar yadda kafar watsa labarai ta Arab News ta ruwaito.

No comments

Powered by Blogger.