Masu tiyata a Saudiyya sun yi nasarar raba wasu 'yan biyu da aka haifa kan su a haɗe a Misra
Salma da Sarah 'yan kasar Misra da aka haifa kan su a haɗe kuma likitoci a Saudiyya suka yi nasarar raba su.
Wata tawagar masu aikin tiyata a kasar Saudiyya sun yi nasarar raba wasu 'yan biyu daga kasar Misra da aka haifa a hade masu suna Salma da Sarah bayan aikin tiyata da ya kwashe awowi 17 ana yi a Riyadh.
"Ta hanyar tabbatar da umarnin sarki Salman da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, tawagar kwararru masu tiyata sun raba wasu 'yan tagwayen kasar Misra wadanda suke a hade ta bangaren kan su, bayan an yi tiyata mai sarkakiya ta tsawon awonni 17." Kamar yadda cibiyar samar da kayan agaji da tallafi ta sarki Salman ta bayyana a cikin wani jawabi a ranar Alhamis.
An fara tiyatar ne da karfe 8:00 na safe a asibitin yara na King Abdullah Specialist Hospital for Children wanda ya ke a King Abdulaziz Medical City, inda kwararrun likitoci, likitoci na musamman, ma'aikata masu samar da taimako da nas-nas 31 suka yi aikin kamar yadda KSrelief ta shaidawa kafar watsa labarai ta Arab News.
Dakta Abdullah Al-Rabeeah ne ya jagoranci tawagar da ta kunshi ma'aikata daban-daban, wanda kuma mai bayar da shawara ne ga kotun Saudiyya wato Saudi Royal Court kuma babban mai kula da ayyukan KSrelief.
Al-Rabeeah ya bayyana cewa 'yan biyun sun zo Saudiyya ne a ranar 23 ga watan Nuwambar 2021, kuma tawagar kwararrun sun yi masu gwaje-gwajen likitanci da dama.
Ya bayyana cewa tawagar masu yin tiyata wadda Dakta Moatasem Al-Zoubi daga "paediatric neurosurgeon", Dakta Muhammad Al-Fawzan daga "plastic surgery " da kuma Dakta Nizar Al-Zughaibi daga "paediatric anesthesia" ke jagoranta sun yanke shawarar yin tiyatar a lokuta kashi hudu, inda suke barin satuttuka da dama a tsakaninsu, domin su raba kwakwalwarsu da sauran abubuwa da suke iri daya na 'yan biyun.
Bayan haka an yi tiyata hudu domin mikar da fatarsu inda ake bukatar haka ta hanyar yin "plastic surgery", inda tiyatar hudu da aka yi domin raba 'yan biyun ta dauki awowi 57 baki daya, in an da awowi 17 da aka dauka yayin tiyatar karshe.
Dakta Al-Zoubi ya bayyana cewa tiyatar na da sarkakiya a wasu bangarori da ya lissafo wanda hakan ya sa suka yi tiyatar kashi-kashi har hudu domin tabbatar da lafiyar 'yan biyun.
Kungiyar samar da agaji ta Saudiyya a baya ta samar da taimako har sau 130 a lokuta da aka samu 'yan biyu da ke a hade daga kasashe 23 a cikin shekaru 33, kamar yadda Al-Rabeeah ya bayyana.
Ya nuna godiyarsa ga sarki Salman da yarima mai jiran gado kan taimakon da aikin raba 'yan biyu da ke hade ke samu a masarautar, wanda hakan ne ya sa aka cimma wannan nasarar da ba a taba samu ba a baya.
Ya ma yaba da kokarin 'yan uwansa likitoci kan kokarinsu wajen samun nasarar tiyatar.
Mahaifan 'yan biyun sun nuna godiyarsu da yabawarsu ga sarki Salman da yarima mai jiran gado kan tiyatar da kuma samar da taimakon da ake bukata, tare da yabawa ga irin ayyukan jin kai da masarautar ke yi.
Post a Comment