Header Ads

GAMAYYAR MABIYA AHLUL BAITI SUN KAIWA SHUGABAN JAM'IYYAR APC TA JIHAR KANO ZIYARA

Daga Muhammad Kabir Sakafa, kano
      Da yammacin jiya Asabar 17/9/22 gamayyar mabiya da masoya ahlul baiti (as) wadda aka fi sani a turance da suna 'Ahulul bait united developed association, kano' ta kaiwa shugaban jam'iyyar APC dan sarki jikan sarki mai girma Abdullahi Abbas ziyarar ban girma a ofishin sa dake kano.
     Tawagar masu ziyarar wadda ta kunshi dukkan wakilai na mu'assasoshi na mabiya ahlul baiti tare da wakilai daga kungiyar sharifai da ashabul kahfi da sauran masoya ahlulbait (as) ne. Bayan bude taro da addu'a sai aka gabatar da shugaban wannan gamayyar mai girma dan majalisar jihar kano mai wakiltar kananan hukumomin kunchi da tsanyawa honorable Garba Ya'u gwarmai (dambu mai hawa biyu) inda yayi takaitaccen bayani a kan ita wannan gamayyar, yace "ita wannan gamayya ce da ta kunshi dukkannin bangarori na mabiya ahlul bait da masoyan su wanda aka fi sani da 'yan shi'a wadda a kalla kowacce mu'assasa da wakilanta a wannan ziyara sannan suna da mabiya masu dimbin yawa a karkashin ta, kuma an kafa ta ne domin hadin kai na mabiya da masoya ahlul baiti tare kusantar junan su sannan da tunkarar kalubalen da ke gaban mu na harkokin siyasa saboda samun fahimtar juna sosai a tsakanin shugabannin siyasa domin rage kaifin rashin wannan fahimta, sannan da bayar da gudummawa wajen zaben dan takarar da muke gani da zaton zai bamu damar gudanar da fahimtar mu ta akida idan yaci zabe kamar yadda ake baiwa kowacce fahimta dama, haka nan ita wannan gamayyar ba wai iya jihar kano bace gamayya ce da take ta kasa baki daya domin tana da rassa a mafiya jihohin kasar nan ciki harda birnin tarayyar Abuja domin kwanan nan ma mun gabatar da taro na kasa a Abuja a karo na biyu da dukkan wakilai na kasa, sannan muna da shirin hada jama'ar mu don yin gangami na akalla dubunnin membobin na ita wannan gamayyar zalla nan gaba kadan".

      Mai jawabi na biyu a wajen ziyarar shine honorable Adamu kabiru wanda tsohon dan takara ne a zabukan da suka gabata kuma gogaggen dan siyasa shima ya yi dan takitaccen bayani a kan makasudin ziyarar inda yace "yana cikin makasudin ziyarar shine gabatar da kai ga shugaban jam'iyya kafin ziyarar wannan gamayya ga yan takarkaru a matakin farko domin da zarar wannan ziyarar ta karbu a wajen shugaban jam'iyya to ta karbu ga dan takarar gwamna da mataimakin sa na wannan jam'iyya domin shine matakin farko, sannan mu shelanta cewa zamu bayar da gudummawar mu wajen zabuka masu zuwa matukar zamu sami 'yancin gudanar da akidar mu ba tare da tsangwama da rashin aminci tare takurawa ba kamar yadda tsarin mulki ya baiwa kowa damar sa", sannan ya karkare jawabin sa da mika godiyar gamayyar saboda samun damar baiwa membobi kulawa wajen yankar katin kuri'a ana dab da rufewa da gwamnati ta yi a fadin jihar kano ta inda aka samu adadin membobin gamayyar suka sami damar mallakar katin zaben".
       A nasa jawabin mai girma sgugaban jam'iyyar APC Alhaji Abdullahi Abbas cewa yayi "yaji dadi da wannan gamayyar sannan su basu da rashin jituwa illa iyaka rashin fahimtar juna da ake yi sakamakon rashin haduwa da samun takarrubi a tsakanin gwamnati da yan shiar, to amma wannan gamayyar zata samar da hakan tare da kore wancan rashin fahimtar da ke tsakani, sannan ya kawo misalsalun wasu abubuwa da suka faru na rashin fahimta da bangaren yan shi'a a garin kano a lokacin da yake kwamishinan muhalli na jiha wajen fita a ranakun asabar din da ake tsabtar muhalli a karshen wata inda yace sai da ya nemi ganin shugaban yan shi'a na kano a wancan lokaci ya kuma bashi lokaci yaje har gida kuma aka samu kyakkyawar fahimta wanda daga nan wannan matsalar bata sake afkuwa ba, wanda hakan ya nuna tasirin shugabanni shi'a a kan mabiyan su, kuma muna shaida muku matukar an bada gudummawa gwamnati ta dawo to mun yi alkawarin kare akida da mutuncin ku tare da samun 'yanci tunda shi dan siyasa ba ya raina adadin kuri'a komai kankantar ta, sannan ko su malaman da ake tare da su batu ne na kuri' a". Sannan ya kara da cewa "hatta ita kanta wannan ziyarar da kuka kawo mai girma gwamna ya san zaku kawo ta domin na shida masa kuma yaji dadi da yin hakan".
     Daga cikin wadanda suka yi takaitaccen tsokaci a wajen sun hada da tsohon dan takarar dan majalisar jiha a karamar hukumar takai honorable Hassan Aqwa da honorable yakubu daga karamar hukumar birni sai jawabin godiya da rufe taro da addu'a daga bakin Sheikh khidir lawal.

No comments

Powered by Blogger.