Ambaliya mai zuwa: Minista Sadiya ta gargaɗi jihohi da ƙananan hukumomi kan aikin kwashe jama'a
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta
faɗakar da gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi da ma shugabannin jama'a,
musamman a jihohin Anambara, Delta, Kuros Riba, Ribas da Bayelsa, cewa ambaliyar
ruwa na nan tafe a cikin makwanni masu zuwa, sannan ta yi kira a gare su da su
shirya wa aikin kwashe jama'ar da ke zaune a yankuna da hanyoyin da ruwan ke bi.
Ministar ta faɗi haka ne a taron da ta yi da manema labarai a ranar Lahadi a
Abuja domin bayyana masu ƙoƙarin da gwamnati ke yi na rage raɗaɗin bala'in
ambaliya a ƙasar nan, wanda ta ce babbar matsala ce.
Hajiya Sadiya ta ce duk da
gagarumin ƙoƙarin da ake yi na kauce wa matsalolin ambaliyar wannan shekarar ta
2022 kamar yadda Hukumar Nazarin Yanayi ta Nijeriya ta hango zai faru,
gwamnatocin jihohi da dama ba su yi wani shiri dangane da ambaliyar ba, wanda
hakan ya jawo babbar asarar rayuka da ɓarnata dukiyoyi.
Ta ce: “Abin baƙin ciki
ne a ce an rasa rayuka sama da 603 ya zuwa yau 16 ga Oktoba, 2022. Jimillar
mutum 1,302,589 su ka gudu daga muhallin su, mutum 2,504.095 abin ya shafa baki
ɗaya, mutum 2,407 sun ji rauni, jimillar gidaje 82,053 sun rushe baki ɗaya,
yayin da guda 121,318 su ka lalace a wasu sassa nasu.
Hekta 108,392 ta gonaki ta
lalace a wasu sassa yayin da hekta 332,327 ta salwanta baki ɗaya, wanda ya haɗa
da hanyoyi da yawa da sauran muhimman ababen more rayuwa. “A yayin da mu ke
alhinin haɗarin nan mai ban takaici na kifewar kwale-kwale da ya faru a Jihar
Anambara da sauran wurare, don Allah mu lura da cewa ba wai gaba ɗaya ba mu san
abin da ke faruwa ba ne domin kuwa Hukumomin Nazarin Yanayi su na ta gargaɗin
cewa jihohi irin su Anambara, Delta, Kuros Riba, Ribas da Bayelsa su na
fuskantar barazanar faɗawa bala'in ambaliya har zuwa ƙarshen Nuwamba. “Mu na
kira ga gwamnatocin waɗannan jihohin da ƙananan hukumomi da al'ummomi da su
shirya wa kwashe mutanen da ke zaune a wuraren da ambaliya ke bi zuwa wurare
masu tudu, su samar da tantuna da kayan agaji, da ruwan sha da kuma kayan magani
saboda yiwuwar ɓarkewar annobar cututtuka.”
Bayan haka, wata babbar tawaga da
ma'aikatar ta kafa ya na nan ya na shirin kai wa gwamnonin jihohi ziyara domin
ganawa da su kan su ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa shirin su na tunkarar matsalar
ambaliyar kamar dai yadda aka tsara a Shirin Gaggawa kan Ambaliya na Ƙasa, wato
'National Flood Emergency Preparedness and Response Plan'.
Ana sa ran masu ruwa
da tsaki a lamarin za su yi aikin da aka rataya masu a wuyan su domin hana
aukuwar mace-mace saboda ambaliya ko wasu cututtuka da ke da alaƙa da rashin
lafiya daga al'amarin wanda ka iya faruwa. Bugu da ƙari, Babban Sakataren
ma'aikatar, Dakta Nasir Sani Gwarzo, zai jagoranci wata tawaga zuwa ƙasar Kamaru
a watan gobe domin su tattauna da hukumomin ƙasar kan batun buɗe dam ɗin Lagdo
jefi-jefi.
Haka kuma kwanan nan za a aiwatar da Shirin Gaggawa kan Ambaliya na
Ƙasa domin a samu daidaito wajen aikin tunkarar matsalar ambaliya, sannan a
samar da hanyar gudanar da aikin kula da ambaliya a matakan ƙasa baki ɗaya daga
sama har zuwa ƙasa. Bayan haka, kusan dukkan jihohi 36 da Gundumar Birnin
Tarayya sun karɓi kayan abinci da waɗanda ba na abinci ba domin rage matsaloli
daban-daban na bala'in ambaliyar. Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta
Ƙasa (NEMA), Alhaji Mustapha Habib Ahmed, shi ne ya bayyana haka a wajen taron
da ministar ta yi da manema labarai.
Ya ce: “Labarin da wasu ke yaɗawa cewa wai
ba a ga abin da Gwamnatin Tarayya ta yi a jihohin da ambaliya ta shafa ba ƙarya
ne. Mu na nan a kowace jiha ta ƙasar nan. Mun kai kayan agaji a kowace jiha ta
ƙasar nan.
"Kuma mu na gode wa Babban Kwamandan Askarawa kuma Shugaban Ƙasa
Muhammadu Buhari da mai girma Minista. "Za mu ci gaba da yin ƙoƙarin mu wajen
sama wa ƙasar nan agaji."
Waɗanda su ka halarci taron dai sun haɗa da Babban
Sakataren ma'aikatar, Dakta Nasir Sani Gwarzo, da shugabannin hukumomi da
daraktocin ma'aikatar. Hoto: Minista Sadiya Umar Farouq ta na gabatar da jawabi
ga manema labarai
Post a Comment