Header Ads

Hare-hare: Shugaban INEC ya lissafa asarar da aka yi, da hanyoyin samun mafita


Farfesa Mahmood Yakubu yana jawabi a taron

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukunta masu kai hare-hare da lalata dukiya da kayayyakin hukumar a faɗin ƙasar nan cikin hanzari ita ce hanyar da za a bi a magance matsalar. 

Yakubu ya faɗi haka ne a lokacin buɗe taron kwana biyu don buɗe idon Zaunannun Kwamishinonin Zaɓen hukumar (RECs) da aka yi a Legas a ranar Laraba. 

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Hukumar Cigaban Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ita ce ta ɗauki nauyin shirya taron.

A jawabin sa na buɗe taron, Yakubu ya bayyana cewa a cikin watanni huɗu da su ka gabata, wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kai hare-hare a ofisoshin hukumar da ke ƙananan hukumomi biyar na ƙasar nan.

A cewar sa, muhimman kayayyaki da dukiyoyi sun salwanta a lokacin waɗannan hare-haren, don haka ya kamata a magance abin da ke faruwa a cikin gaggawa.

Ya ce: “Waɗannan kayayyakin sun haɗa da jimillar akwatunan zaɓe guda 1,992, da rumfunan zaɓe 399 da janaretocin ba da wuta guda 22, da kuma dubban katinan zaɓe da ba a kai ga karɓa ba, da wasu kayan.

“Tilas ne a dakatar da waɗannan hare-haren kuma a kai masu aikata su kotu. Aikin mu shi ne mu gudanar da zaɓe. Hanyar da ta fi dacewa domin magance matsalar ita ce a kama masu kai hare-haren a gurfanar da su a kotu.

“Babban maganin matsalar shi ne a kama ɓata-garin a hukunta su saboda 'yan iska da masu ƙone-ƙone su daina tunanin cewa an amince da aikin assha a ƙasar mu. A gaskiya, abin baƙin ciki ne a ce ana yin wannan a lokacin da zaɓuɓɓuka ke ƙaratowa.

“Sai dai kuma, ina so in tabbatar wa da 'yan Nijeriya cewa za mu ga bayan waɗannan hare-haren, za a maye gurbin waɗannan kayan. To amma akwai iyakar yadda za mu iya ci gaba da maye gurbin kayayyakin da mu ka rasa a yayin da ya rage mana kwana 86 kacal kafin ranar babban zaɓe.”

A cewar sa, hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma da dukkan mutanen kirki 'yan Nijeriya domin hana hare-haren.

Ya ce INEC ta duƙufa wajen tabbatar da cewa babu abin da zai hana a gudanar da zaɓuɓɓuka kamar yadda aka tsara, "kuma muradin al'ummar Nijeriya zai cika. Wannan shi ne mu ke ƙara tabbatar wa da 'yan Nijeriya.”

A game da taron buɗe idon, Yakubu ya ce wani ɓangare ne na shirye-shiryen da ake yi domin manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023.

Ya ce: “Mu na yin taro ne da dukkan Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe domin mu na sane da cewa an rantsar da 19 daga cikin su kimanin mako huɗu da su ka gabata.

“Mun yi tunanin cewa ya kamata a shirya masu taron buɗe ido domin su fahimci hanyoyi da ƙa'idojin aiki saboda za a yi zaɓe nan da kwana 86.”

Shugaban na INEC ya ce taron buɗe idon zai kuma mai da hankali ga ainihin ƙa'idar aiki kan karɓar katittikan zaɓe, da ƙa'idojin rarraba masu zaɓe zuwa rumfunan zaɓe, da tsarin yadda ake raba kayan zaɓe, da dokokin ɗabi'u da halayyar membobi da jami'ai da ma'aikatan hukumar.

Yakubu ya ce za a rarraba kwafe-kwafe na dokokin ɗabi'ar membobi da jami'ai da ma'aikatan hukumar ga kowa da kowa.

Ya ƙara da cewa: “Ina so in nanata cewa samun nasarar mu a ƙarshe ya dogara ne kan mutuncin mu. Tilas mu zama ba mu kowane ɓangare kuma ba mu goyon bayan kowa.

“Hukumar ba jam'iyyar siyasa ba ce. Hukumar ba ta da 'yan takara a zaɓuɓɓukan da ke tafe.

"Dukkan jam'iyyun siyasa daidai su ke da juna a wajen hukumar. Zaɓi ya rage wa 'yan Nijeriya, wato masu zaɓe.

“Aikin mu shi ne mu tabbatar da darajar ƙuri'u, ba daɗi ba ƙari.”

Da ya ke magana kan ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa wai mutum zai iya kaɗa ƙuri'a ba tare da katin zaɓe ba a ranar zaɓe, Yakubu ya bayyana wannan maganar da cewa “ko kaɗan ba gaskiya ba ce,” ya na cewa, “kafin kowane mutum ya yi zaɓe, sai ya kasance ya yi rajista a matsayin mai zaɓe, kuma an ba shi katin zaɓe.

“Tun tuni hukumar ta fito da dokar cewa ‘ba katin zaɓe, ba zaɓe'.  Babu abin da ya canza. Dokar ce ta tanadar da hakan, saboda haka in aka yi wani abu daban to an karya dokar.

“Ina kira ga 'yan Nijeriya da su yi watsi da irin waɗannan shaci-faɗin cewa wai mutum zai iya kaɗa ƙuri'a a ranar zaɓe ba tare da katin zaɓe ba.”

Da ya ke yaba wa UNDP saboda ɗaukar nauyin shirya taron da ta yi, Yakubu ya ce haɗin gwiwar da ta daɗe ta na yi da INEC ya jima kuma ya taimaka gaya wajen yauƙaƙa cigaban da ake samu a wajen harkokin shirya zaɓe.

A saƙon sa na fatan alheri, Mista Deryck Fritz, wanda shi ne babban mashawarcin UNDP, ya yi kira ga kwamishinonin da su dage sosai wajen aiwatar da tsare-tsaren hukumar kuma su kasance kan gaba wajen masu magance matsaloli idan sun taso.

Ya ce su ne za su sa ido kan aiwatar da dukkan ayyukan da su ka rataya a wuyan hukumar kamar yadda aka ba su amana. 

Ya ce: "Ku ne waɗanda za su yi aiki ba tare da goyon baya ba da 'yan siyasa.

“Ku ne waɗanda za su yi aiki da abokan hulɗa da ke yankunan ku da ƙungiyoyin 'yan sa kai, da  hukumomin jiha, da goyon bayan ƙungiyoyin sufuri, da sauran masu ayyuka, da 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

“A wannan waƙati na gasar Kofin Duniya, ana tuna mana da cewa zaɓuɓɓuka masu nasara, kamar gasannin ƙwallon ƙwafa masu nasara, su na samuwa ne sakamakon haɗin kai tare da aiki tare.” 

Fritz ya ce a yadda wasu ke kallon abin, wannan cigaba da ake samu wajen aikin shirya zaɓe ba zai taɓa sauyawa ba, amma kamar yadda ya ke faruwa a kowane zaɓe, akwai matsalolin da ka taso, kamar siyasar kasuwa da kuma matsalolin tsaro.

Ya ce irin waɗannan ƙalubale za su jarraba ƙarfin hanyoyi da dokokin INEC, har ma da sadaukarwar ma'aikatan ta.

Ya ce tsarin dimokiraɗiyya, a sassa da dama na duniya, ya na fuskantar barazana, ya ƙara da cewa samar da tsari mai ƙarfi ne zai yi maganin wannan barazanar.

Ya ce, “Idan kuma ana kokwanto kan tsarin da ke akwai game da ɗabi'ar tsarin, ko ana zargin masu gudanar da zaɓe, ko ma a ce an yi murɗiya, ya na da muhimmanci ya kasance akwai tsari mai nagarta wanda aka amince da shi da zai tunkari waɗannan matsalolin, a madadin a yi tarzomar zaɓe da rikicin siyasa.

“INEC a matsayin ta na hukumar da tsarin mulki ya ba alhaki, tilas ta kasance kuma a ga ta kasance ba ta nuna wariya a matsayin ta na alƙalin zaɓe.”

Dukkan Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe na INEC da manyan ma'aikatan hukumar sun halarci taron.

Kwamishinonin zabe a taron

No comments

Powered by Blogger.