Header Ads

Jama'a sun yi tir da hukuncin da Kotu ta yanke wa Sheikh Abduljabbar na hukuncin kisa ta hanyar rataya

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara 

Babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta ce ta same shi da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.

An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same shi da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su.

Sai dai a wani jin ra'ayin jama'a da Wakilinmu ya gudanar, akasarin jama'a na ganin cewa, duba da yadda shari'ar ta gudana, an sanya son rai a ciki, don haka ba a yi adalci ba.

Daga cikin tuhumar da ake yi masa akwai zargin tayar da tarzoma a jihar Kano ta hanyar wa'azinsa.

Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari'a Sarki Yola ya ɗage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.

Bayan ɗan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.

Sai dai kafin a tafi hutun, Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya yi magana ta ƙarshe, inda ya ce bai san lauyan da ke kare shi ba, kuma ba ya neman afuwa, saboda, a cewarsa, bai aikata laifi ba kuma ya nemi a gaggauta yanke masa hukunci.

Mai Shari'a Sarki Yola ya ce, malamin yana da kwana 30 don ɗaukaka ƙara idan bai gamsu da hukuncin ba.

A ranar Juma'a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama'a, zargin da ya sha musantawa.

Shaikh Abduljabbar ya gaza kare da'awar da ya yi kan Annabi Muhammadu - Kotu

Cikin iƙirarin da Abduljabbar ya yi a wa'azizzikan da ya sha gabatarwa, wadda kuma ake tuhumar sa a kanta, har da maganar cewa Annabi Muhammadu ya yi ƙwacen mata mai suna Safiyya daga wani sahabinsa.

Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya ce malamin "ya gaza kare wannan da'awa ko iƙirari da ya yi da karɓaɓɓun hujjoji".

Ɗaya daga cikin lauyoyin gwamnatin Kano, Farfesa Mamman Lawan Yusufari, ya faɗa wa BBC Hausa cewa sun gabatar da shaidu huɗu don tabbatar da laifin da suke zargin malamin da shi.

Kotu ta ƙwace litattafan Abduljabbar
Ƙari a kan hukuncin kisa da kotun ta yanke, ta kuma ba da umarnin ƙwace dukkan litattafan da Sheikh Abduljabbar ya gabatar don kare kan sa da su.

An bayyana litattafan da suka kai kusan 200, waɗanda shehin malamin ya yi amfani da su yayin zaman muƙabalar da aka gudanar a watan Yulin 2021 da zimmar kare da'awarsa.

Kotun ta ba da umarnin a miƙa litattafan ga Babban Ɗakin Karatu na Jihar Kano.

Bugu da ƙari, kotu ta haramta saka karatun malamin a dukkan kafofin yaɗa labarai na jihar, tare da bai wa gwamnati shawarar ta ɗauki "duk matakin da ya dace" kan wanda ya saɓa umarnin.

Haka nan, ta ba da umarnin rufe masallatan Abduljabbar biyu.

BBC ta yi yunƙurin jin ta bakin lauyan malamin, amma ba mu samu damar yin hakan ba.

Muhimman abubuwan da suka faru yayin hukuncin shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara.

Aliyu Samba

1. Kotu ta yi watsi da sukar da lauyoyin Malam Abduljabbar suka yi a kan ingancin tuhuma tun daga farkon shari'ar zuwa jawabin ƙarshe da aka gabatar a rubuce.

2. Kotu ta gamsu cewa dukkan kalaman da ake zargin Malam Abduljabbar Kabara da furta su, shi ne ya ƙirƙire su. 

3. Kotu ta karɓi shedun da masu gabatar da ƙara suka kawo gaban kotun. 

4. Kotu tana ganin cewa, korewar da Malam Abduljabbar ya yi ba za ta kuɓutar da shi daga hukuncin da doka ta tanada ba a kan wanda ya furta kalaman ɓatanci ga Annabi SAWA.

5. Kotu ta yi watsi da duk wani bayanin da Malam Abduljabbar ya yi wanda bai da alaƙa da tuhumar da ke gaban ta.

6. Kotu ta ce Malam Abduljabbar yana fassara kalmomi ba tare da la'akari da siyaƙin da maganar ta zo ba, kuma ba ya fito ma'ana kyakkyawa sai mummuna a kan hadisai.

7. Kotu ta kore fassarorin da Malam Abduljabbar Kabara ya yi, ta kuma bayyana cewa fassarorin Farfesa Ahmad Murtala sune suka fi daidai da ma'anar hadisan, sannan kuma ta tabbatar da cewa ta karɓe shi a matsayin ƙwararre a fannin hadisi.

8. Kotu ta ce ba ta gamsu Malam Abduljabbar Mujtahidi ne muɗlaƙi kuma ba ta yarda da  ƙwarewar sa ba. 

9. Kotu ta yi hukuncin cewa ta samu Abduljabbar Kabara da laifi kamar haka;

A. Ƙage wa Ma'aikin Allah da jafa'i takan ƙirƙira masa kalmar fyade don cin mutuncin Ma'aiki SAWA wanda ya saɓa da sashe na 382 (b) Shari'a Penal Code.

B.Ƙage wa Ma'aikin Allah da jafa'i takan ƙirƙira masa kalmar ƙwace don cin mutuncin Ma'aiki SAWA wanda ya saɓa da sashe na 382 (b) Shari'a Penal Code.

C. Ƙage wa Ma'aikin Allah da jafa'i takan ƙirƙira masa kalmar Auren dole don cin mutuncin Ma'aiki SAWA wanda ya saɓa da sashe na 382 (b) Shari'a Penal Code.

D. Ƙage wa maaikin Allah da jafa'i takan ƙirƙira masa kalmar Biyan buƙatar tsakanin namiji da mace don cin mutuncin Ma'aiki SAWA wanda ya saɓa da sashe na 382 (b) sharia Penal Code.

10. Kotu ta ba wa wanda yake riƙa wa lauyan da ke kare wanda ake ƙara dama ko yana da wata magana. Lauyan ya ce yana roƙon a sassauta wa wanda ake ƙara wajen hukunci kasancewar sa mai iyali, kuma magidanci, sannan kuma ya yi maganganun da ya yi ne bisa kuskure da rashin fahimta.

11. Malam Abduljabbar Kabara ya ce shi bai san wannan lauya ba, kuma ba wakiltar sa yake ba, kuma ba da yawun sa yake magana ba. Sai dai kotu bayan ta saurari wannan koke na Malam Abduljabbar, ta ci gaba da sauraron roƙon da lauyan yake yi a madadin Malam Abduljabbar Kabara. 

13. Kotu ta ce ita ta gamsu wannan lauya wakiltar Malam Abduljabbar yake, domin wanda kotu ta wakilta ne ya aiko shi.

14. Malam Abduljabbar a jawabin sa na ƙarshe ya ce "bayan na saurari duk abin da ka faɗa na juya duk hujjoji na sama da ƙasa, ka ƙaga min zagin Annabi SAWA..."    A nan ne lauyan masu gabatar da ƙara, Shu'aibu Sa'idu SAN ya ce; "Wannan magana da yake ba magana ce da zai faɗi wannan maganganu a kotu ba. Ai damar da aka ba shi, na ya nemi sassauci ne ba na muƙabala a Shari'a ba, kuma ba lokaci ne na ya  ƙalubalanci hukuncin da kotu ta yi ba. Ina roƙon kotu ta datse shi.''

15. Kotu ta yi umarnin a bar Malamin ya ci gaba da bayaninsa, ya ci gaba da cewa; 

''Ni ba na neman sassauci a kan wannan laifi da ban yi ba, ina ba wa masoyana hakuri, kar su samu damuwa kan tafiya ta lahira. Zan yi mutuwa ta girma, kuma ba na neman kai Ibrahim Sarki ka yi min sassauci. Kuma a gaggauta yi min hukuncin nan. Kalami na na ƙarshe kenan, '' in ji Sheikh Abduljabbar.

Alkali Ibrahim Sarki Yola

No comments

Powered by Blogger.