Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ceto yara biyu, tare da kama matasan da suka yi garkuwa da su
To sai dai bayan samun rahoton, kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Mamman Dauda tare da hadin gwiwar SP Muhammad, wanda shi ke shugabantar rundunar yaki da garkuwa da mutane tare da tawagar shi sun ceto yaran sun kuma yi nasarar kama batagarin.
Nura Auwal da Abubakar Lawal, 'yan shekarar 22 da haihuwa da ake zargi da aikata wannan laifi tuni suka amsa laifinsu na hada kai wajen yin garkuwa da yaran domin neman kudin fansa bayan da suka shiga hannu yayin da aka fara gudanar da bincike cikin al'amarin.
Ana dai sa ran ba da dadewa ba za a kai su kotu domin fuskantar hukunci bayan kammala bincike.
Duk da cewa yaran da aka ceto din a cikin wani kangon gini suke, to amma ba wata cutuwa a tare da su.
Post a Comment