Header Ads

CBN ya yi amai ya lashe! Ya ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin kuɗi


Babban bankin Najeriya CBN ya sanar da ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin kuɗi zuwa 10 ga watan Fabirairu, abin da masharhanta suka ce tamkar amai ka lashe ne.

Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Gwamnan ya ce ya zuwa yanzu CBN ya karɓi naira tiriliyan 1.9 na tsofaffin kuɗi, saura kuma naira biliyan 900 ya kammala karɓar tsofaffin kuɗaɗe.

Ya yi bayanin cewa sai da CBN ya nemi sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari domin ɗage wa’adin karɓar tsofaffin kuɗin, wanda kuma ya amince a ƙara wa’adin da kwanaki 10.

“Sakamakon halin da ake ciki, mun nemi umarnin kuma mun samu daga shugaban ƙasa kamar haka: ƙarin kwanki 10 na karɓar tsofaffin kuɗi daga 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan gobe na Fabirairu, za a ci gaba da karɓar kuɗin daga hannun ‘yan Najeriya a hukumance,” in ji sanarwar.

No comments

Powered by Blogger.