Header Ads

BAYANI A TAƘAICE KAN GWAJE GWAJEN DA AKE SON YI KAFIN AURE

BAYANI A TAƘAICE KAN GWAJE GWAJEN DA AKE SON YI KAFIN AURE
Daga Saifullah Ningi

Gwaje-gwaje mafi muhimmanci sune Genotype, HBV, RVST, da kuma PT ga mata.

1. Genotype shi gwaji ne da ake yi domin a gane kalar jinin ma'aurata domin gudun samun zuriya mai Sikila. Gwajin sun kasu gida uku, akwai AA, AS, SS. 
Lokacin da akayi gwaji aka samu AA + AA to auren is very excellent, AA + AS shima ba matsala. Amma da an samu AS + AS to hakuri shi yafi domin cikin ƴaƴan za a iya samun mai sikila, balle kuma ayi maganar AS+ SS ko SS + SS.

2. HBV (wato Hepatitis B. Virus) shi kuma in an samu ɗaya yana dashi ɗaya bai dashi to ana iya yiwa wanda bai dashi Immunization a ɗaura aure kuma ba tare da an samu matsala ba a zamantakewa. 

3. RVST (Retro Viral Screening Test wanda aka fi sani da HIV) shi kuma gwajinsa yakan ɗauki mataki uku ne aƙalla. Na farko ana yi da Stat Pak, in ya gwada babu sai ayi da Determine shima in babu sai aje na ƙarshe ayi da Uni-Gold, kuma so samu gwajin a ɗauki lokaci anayi kamar sau uku. amma yanzu in kaje da stat pak kawai ake yi ba a tsayawa abi sauran matakan, wani ma ranar aurensa yake zuwa a gwada. 

4. PT test: wato Pregnancy Test shi kuma wannan dama sananne, ana gwajin sane domin duba yiwuwar samuwar ciki ko akasin shi. Shi dama wanann mata sukan ma saya suyi a gidajensu. Domin samun sakamako mai kyau an so ayi amfani da fitsarin farko da aka yi da safiya.

Wannan a taƙaice kenan.
Allah ya datar damu 

Saifullah Ningi, Microbiologist ne.

No comments

Powered by Blogger.