Header Ads

Za a rika daukar dalibai da talakawa a mota kyauta tare da ba su tallafin kudi a jihar Kwara

Gwamnan jihar Kwara: Sai yanzu da zabe ya kunno kai?

A cikin wata sanarwa wadda kakakin gwamnan jihar Kwara, Rafiu Ajakaye, ya fitar a ranar Alhamis, kakakin ya bayyana cewa gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq, ya umarci hukumar shirin bunkasa rayuwar jama'a ta jihar KWASSIP (Kwara State Social Investment Programme) da ta gaggauta tsara yadda za a gudanar da wani muhimmin shiri domin saukakawa jama'a radadin wahalar karancin mai da na naira.

A cikin shirin, gwamnan jihar dai ya amince ne da a rika daukar dalubai, 'yan fansho da sauran jama'a talakawa masu rauni kyauta a motocin haya na bas.

Haka kuma gwamnan jihar ya amince da a rika bayar da taimakon kudi ga matan da mazansu suka rasu, 'yan fansho, masu motocin sufuri, kananan manoma, 'yan kasuwa da sauran talakawa a jihar, inda za a rika tura masu da kudaden.

Kamar yadda kakakin ya bayyana, hakazalika gwamnan ya amince da a sanya bas-bas na kyauta a wasu hanyoyi wadanda dalubai da malaman manyan makarantu suka fi bi a babban birnin jihar, inda aka fi shan wuyar rashin man.

No comments

Powered by Blogger.