Header Ads

An yi muzaharorin Allah wadai da El-Rufai


Masallacin kofar gidan marigayi Alhaji Hamidu Danlami da Elrufa'i ya rusa

'Yan'uwa musulmi a Nijeriya a ranar Juma'a sun hau kan tituna domin yin Allah wadai da mummunan aikin tsohon gwamnan jihar Kaduna na rushe kadarori mallakin 'yan'uwa musulmi wadanda suka hada da asibitoci, makarantu da gidaje.

A jihar Bauchi, masu muzahara sun dauko hotunan gwamna Nasiru El-Rufai tare da soke shi, da rubuce-rubuce da ke dauke da alluna da aka rubuta, "Muna Allah wadai da ayyukan El-Rufai na ta'addanci, Allah Ka yi hukunci kan El-Rufai da kuma kamar Gaza kamar Kaduna."  

Daya daga cikin masu muzaharar, Khadija Adamu ta shaidawa Iran Press cewa, "Mun fito ne domin mu yi Allah wadai da ayyukan gwamna El-Rufai na ta'addanci na rushe mana asibitoci, makarantu da sauran gine-gine. Muna ma kira ga kotun duniya (ICC) da ta dauki babban mataki a kan Nasiru El-Rufai."

Wani daga cikin masu muzaharar, Haj Muhammad Bununu, ya bayyana cewa irin zaluncin gwamnan jihar Kaduna ya yi kama da ta'addancin Isra'ila kan mutanen Falasdinu.

"Muna kira ga duka musulmai na duniya da masu fafutika da su yi Allah wadai da ayyukan El-Rufai na ta'addanci wadanda suke kama da irin wadanda Isra'ila ke amfani da su kan mutanen Falasdinu da ke Gaza." 

A ranar Laraba, kungiyar Amnesty International ta fitar da wani jawabi kan yadda al'amarin ya ke tare da yin Allah wadai da zaluncin El-Rufai.

"Amnesty International na yin kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta tattauna da duk wadanda wannan al'amari ya shafa domin samun wata hanya da ta fi dacewa ba fitar da su daga muhallai ba. Samun hanyar da ta fi dacewa da kuma diyya dole ne a samar da su ga wadanda al'amarin ya shafa." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin da kungiyar ta fitar.

A dai ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari zai mika mulki ga sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a yayin da kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, zai mika kujerar mulkin jihar ta Kaduna ga sabon gwamna, Uba Sani.

A cikin gwamnoni 36 da ke Nijeriya, Nasiru El-Rufai ne kawai ya kaddamar da hare-hare a kan harkar musulunci a Nijeriya wadda ke neman zaman lafiya, hakan kuwa ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama, ciki har da yara da mata.

A dai satin da ya gabata ne gwamnan jihar ta Kaduna ya fara rushe-rushen kadarorin waÉ—anda aka fi kira 'yan shi'a da ke Kaduna da Zariya.

No comments

Powered by Blogger.